✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar FRSC, wannan tarar  ta yi tsanani

A Juma’ar da ta gabata ce, Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta bayyana cewa daga badi, za ta fara cin tarar masu saba dokar fitilar…

A Juma’ar da ta gabata ce, Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta bayyana cewa daga badi, za ta fara cin tarar masu saba dokar fitilar da take ba da hannu a kan hanya Naira Dubu  50, ga duk wanda ya karya doka, kudin dai ya kai ninki 12 idan aka kwatanta da wanda ake biya a baya na Naira dubu hudu. Hukumar ta ce saba ka’idojin hanya ya zama ruwan dare, Shugaban Hukumar FRSC Mista Boboye Oyeyemi, ya ce shirin kara kudin tarar dama can yana nan, tun kafin a kafa kwamitin harajin kar-ta-kwana.

Da yake bayani a wajen taron wata na farko da hukumar ta shirya tare da masu ruwa-da-tsaki da hadin gwiwar Hukumar  Kare Hakkin Abokan Hulda ta Kasa (CPC), Shugaban ya ce, mutanenmu za su ci gaba da kamAwa da kuma cin tarar duk direbobin da suke tuki sannan suke amfani da wayar salula. Oyeyemi,  ya yi karin haske a kan yadda masu karya doka suke amfani da lauyoyinsu wajen yi wa hukumar barazanar gurfanar da ita a gaban kotu. Ya ce a yanzu hukumar tana da lauyoyi 120, sannan ya yi alkawarin sake dibar wadansu domin su tunkari barazanar da direbobi suke yi musu.

Wannan ba shi ba ne karo na farko da Hukumar FRSC ta dauki matakin kara yawan tarar da take cin masu saba ka’ida ba. A cikin watan Oktoban bara hukumar ta yi kari ga masu saba ka’ida daga Naira dubu 50 zuwa dubu 100 ga masu tafiya suna aikewa da sakon kar-ta-kwana da kuma masu amsa wayar salula alhali suna cikin tuki. Karin tarar ga direbobi masu tukin ganganci ya zama dole lura da yadda tarar da ake cinsu yanzu ba ta hana su karya doka ba. Matsawa da kuma tilasta wa masu saba doka da hukumar kiyaye hadduran ta ke yi, ya sa wadansu ’yan kasa da dama garzayawa kotu domin neman kariya.

A cikin wata shari’a mai lamba FHC/L//CS/1234/13 a tsakanin  Tope Alabi da FRSC, wanda  Mai shari’a J.T. Tosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Legas  ya yanke ta bayyana cewa Hukumar FRSC ba ta da karfin tirsasawa wajen cin tarar masu ababen hawa, wanda wannan kotu ba ta da hurumin yanke wannan hukunci. Saboda hukuncin wannan kotu ba ya zama doka, sakamakon kararraki da aka shigar gaban Kotun Daukaka Kara ya sha gaban na wannan kotun wanda suka bayyana mabambantan ra’ayi, saboda yawaitar wadannan kararraki ya sa wannan hukuma bayyana nata matakin. Wasu daga cikin irin wadannan shari’o’i sun hada da; Tsakanin FRSC da Emmanuel Ofoegbu da kuma tsakanin FRSC da Okebu  Gideon Esk da kuma Barista Moses Ediru da Hukumar FRSC.

Mun yarda cewa asarar da hadarurruka suke janyowa tana karuwa sosai. Misali a kowace shekara ’yan Najeriya sama da dubu 39 ne suke mutuwa sakamakon hadarin mota. A bara rahoton da aka fitar kan kiyaye hadurra a duniya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kiyasta kayayyakin da ake amfani da su wajen kula da hanya sun kai dubu 39 da 802, sannan an kiyasta ana samun kashi 24.4 a cikin  100, na rahoton  mace-macen da ake  samu, saboda haka wannan hukuma ta kiyaye huddura tana da matukar tasari ga samar da kariya sannan tana da dama a cikin tsarin mulki ta yadda za su tsare duk motocin da suka saba doka da kuma cin tarrarsu. Najeriya kamar sauran kasashen duniya tana da nata kason na gurbatattun direbobi, amma duk da haka wannan hanzarin da aka yi wajen kara yawan wannan tarar ba shi ba ne zai samar da maslaha ga matsalar saba dokokin hanya.  Ya kamata a ce an sake duba dokokin domin gyara su ba daukar wannan tsatsauran mataki ba.

Sanarwar karin tarar da Hukumar FRSC ta yi, ya zo wa mutane da ba-zata kuma wadansu suna mamakin ko da ma Hukumar FRSC tana daya daga cikin hukumomin tattara haraji ne. Haka zalika wannan  tara ko haraji da Hukumar FRSC take yunkurin yi, ya nuna yadda hukumar take kokarin koyi da sauran masu kayan sarki wadanda suke karbar cin hanci a bainar jama’a a kan titunan kasar nan. Lokaci ya yi da FRSC za ta mai da hankali wajen daukar matakan kiyaye haddura ba wai ta mayar da kanta mai tattara haraji ba. Ita kanta tarar Naira 4,000 ya yi yawa lura da yadda ake fama da matsin tattalin arziki. Sannan a ce an mai da ita Naira Dubu 50 yayin da mafi karancin albashi bai wuce Naira dubu 30 ba a wata.

Hukumar Kiyaye Haddura ya kamata a ce su mai da hankali wajen wayar wa direbobi kai wajen kula da kuma illolin da suke tattare da  saba ka’idojin hanya. Ya kamata su kirkiri shirye-shirye a gidajen rediyo da sauran kafafen watsa labari kan aikace-aikacenta  domin jan hankali ga masu amfani da hanyoyi .

Kamar yadda karshen shekara ta kusanto muna jan hankalin masu amfani da hanyoyi (direbobi) su yi tuki cikin natsuwa da  bin doka domin kiyaye aukuwar hadari, Hukumar FRSC ta samo wata hanya da za ta taimaka mata wajen ganin ta aiwatar da aikin da ke kanta.