✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Haraji ta tara Naira tiriliyan 4.63 cikin wata 10

Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa, (FIRS), ta ce ta samu nasasrar tara harajin Naira tiriliyan 4 da biliyan 630 a cikin wata 10 daga…

Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa, (FIRS), ta ce ta samu nasasrar tara harajin Naira tiriliyan 4 da biliyan 630 a cikin wata 10 daga Janairu zuwa Nuwamban bara.

Hukumar FIRS ta bayyana haka ne a cikin wani rahoto da ta mika ga Ma’aikatar Kudi ta Tarayya. Takardun bayanan sun an mika su ne ga Kwamitin Rabon Kudaden gwamnati.

Wannan yana nuni da cewa an samu kashi fiye da 72 cikin 100 na adadin kudaden shiga da aka yi hasashen cewa za a tara a cikin shekarar 2018 da ta kare.

An tara Naira tiriliyan daya daga kudin shigar da ya danganci man fetur, sai kuma harajin da ake dora wa cinikin da kamfanoni ke yi, (CIT) inda aka tara har Naira tiriliyan 1.01.

Akwai kuma harajin BAT, wanda ake dora wa kowane dan Najeriya da ya yi ciniki a shagunan zamani da kantuna ko hulda da banki ko gidajen sayar da abinci, inda aka tara Naira bilyan 776.5 daga kayan da ake sarrafawa a cikin gida. Sai kuma Naira bilyan 223.8 da aka tara daga harajin BAT kan kayan da aka shigo da su daga waje.