✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar INEC ta bai wa Okorocha takardar shaidar cin zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ba da takardar shaidar cin zabe ga tsohon Gwamnan Jihar Imo Mista Rochas Okorocha a matsayin…

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ba da takardar shaidar cin zabe ga tsohon Gwamnan Jihar Imo Mista Rochas Okorocha a matsayin Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma.

Wannan na bisa umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar ne, sai dai Hukumar INEC ta ce za ta daukaka kara a kai. Babban Kwamishinan Watsa Labarai da wayar da kan jama’a kan  jefa kuri’a Barista Festus Okoye ya ce bayan wani taro da kusoshin zartarwa na hukumar suka gudanar a Abuja, hukumar ta ce hukuncin kan iya bai wa ’yan siyasa masu neman mulki kawo cikas ga tsarin gudanar da zabe da kuma yin amfani da sashin shari’a domin biyan bukatunsu. Ya kara da cewa hukumar a ranar Talatar da ta gabata ta duba wasu kudirori 14 da suka hada da hukunce-hukuncen kotuna da umarnin tsare-tsaren zabe da bayar da takardun shaida da kuma janye su.

Tun Farko Hukumar INEC ta hana Okorocha takardar shaidar cin zaben, bisa zargin cewa babban jami’in tattara sakamakon zaben ya bayyana sunansa a matsayin wanda ya lashe zaben ne bisa tursasawa.