✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Kwastam ta bude shafin gurbin daukan ma’aikata 3,200

Shugaban Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya wato (Kwastam) Kanal Hameed Ali (mai ritaya), ya ce hukumar kwastan (NCS) ta bude shafin ta na intanet…

Shugaban Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya wato (Kwastam) Kanal Hameed Ali (mai ritaya), ya ce hukumar kwastan (NCS) ta bude shafin ta na intanet daga karfe 12:00 na safiyar yau Laraba domin baiwa masu sha’awar aiki da hukumar damar nuna sha’awar su ta cike gurbin ma’aikata 3,200.

Mukaddashin mataimakin Kwanturola Janar mai kula da sashen walwalar ma’aikatan, Sanusi Umar, wanda ya wakilci Kanal Hameed, ne ya bayyana hakan ne a jiya Talata, a Abuja.

Sanusi, ya qara da cewa, daukan sabbin ma’aikatan ya biyo bayan amincewar kwamitin zartar wa na gwamnatin tarayya. Za a bude shafin daukar ma’aikatan a cikin makonni uku, ta hanyar shiga shafin (vacancy.customs.gov.ng)