✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar LSBCA ta bayyana dalilan rushewar gini a Surulere

Hukumar Lura da Gine-gine ta Jihar Legas (Lagos State Building Control Agency -LSBCA) ta ce amfani da kayayyakin gini marasa kyau da rashin tsari su…

Wani sashe na ginin da ya rushe a SurulereHukumar Lura da Gine-gine ta Jihar Legas (Lagos State Building Control Agency -LSBCA) ta ce amfani da kayayyakin gini marasa kyau da rashin tsari su ne suka janyo rushewar gini mai hawa biyu da kimanin mutum biyar suka mutu a karshen makon da ya gabata a unguwar Surulere da ke Legas.
Mai magana da yawun hukumar mai suna Abe Adunola ta bayyana cewa  hukumar ta dakatar da ginin, amma maginin ya ci gaba da gini.
Ta ce, “Tun watan Mayun da ya gabata hukumarmu ta dakatar da ginin kuma har an yi masa alamar rushewa, amma sai mai gidan ya yi biris ya ci gaba da ginin inda ya rika amfanin da kayayyaki marasa kyau, kuma ba tare da wani tsari ba. Babu wani kwararre da ke kula da ginin. Wani lokaci ma cikin dare suke yi ginin, ko ranakun karshen mako lokacin da ma’aikata ba sa aiki”.
Ta ci gaba da cewa, “Mun yi iya kokarinmu domin dakatar da ginin, amma bayan mun sanya alamar dakatarwa, sai suka cire suka ci gaba. Kuma mun gano cewa mai ginin ya rika yin amfani da leburorin jeka-na-yi-ka. Ka ga yanzu abin da ya janyo. Za mu dauki matakan da suka kamata don ganin an hukunta mai gidan”.
Shi ma shugaban mazauna unguwar Adeniji da Itire da Ishaga, Tajudeen Bello ya ce duk kokarin da ya yi don dakatar da ginin ya ci tura. “Na yi masa magana cewa ya zama wajibi ya dakatar da ginin, saboda kayan da ake amfani da su ba su da kyau, amma ya ki ji ya ci gaba da gininsa saboda yana ikirarin yana da daurin gindi”.
Ya yi kira ga mazauna unguwannin Surelere su guji kama haya  ko rabar duk ginin da suka ga an sanya masa alamar rusau na hukumar LSBCA.
Ita kuma Hukumar NEMA ta ce ana ci gaba da kwashe baraguzan ginin don gano ko akwai sauran mutanen da suka makale a ciki.