Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Hukumar NAFDAC ta gano gurbataccen manja a Potiskum

Hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) reshen Jihar Yobe  ta yi nasarar gano yadda wasu fataken manja ke sayar da gurbataccen manja a garin Potiskum.
Da ya ke bayanin hakan ga Aminiya a garin Damaturu Kodinetan hukumar a Jihar Yobe, Lawan Musa Dadingelma ya ce hukumarsa ta yi nasarar kame manjan da aka gurbata ne a wani samame da suka kai a babbar kasuwar garin Potiskum inda suka tarar da jarkoki sama da 30 cike da manjan girkin da aka gurbata shi da wasu sinadaran dake da hatsari ga rayuwar al’umma.
Da Aminiya ke tambayarsa akan  irin sinadaran da suka gano tattare da wannan manja da suka kame? Sai ya ce, sun gano wani sinadarin launin ja da masu rina kayan sawa ke amfani da shi don mayar da suturu su koma ga launin ja a cikin manjan inda fataken ke gauraya manjan da wannan sinadarin don manjan ya koma ja jawur don jawo hankalin masu saya da sauran sinadarai masu matukar hatsari.
Kodinetan na (NAFDAC) ya ci gaba da cewar, baya ga kame gurbataccen manjan har ila yau hukumar ta rufe wasu gidajen da ake sarrafa ruwan sha na fiya wota (pure water) da gidajen burodi sama da 7 da suke yin wannan sana’a ba tare da neman izinin hukumar ba.
Ya ce hukumarsa a halin da ake ciki ta daura damarar yin fito- na- fito da duk wadanda ke kokarin sayar da gurbatattun kayayyakin da doka ta hana ga al’umma ta wajen dakile kudurorin su  tare da kwace kayayyakin da duk suka samu tattare da su, sannan za a gurfanar da su a gaban kuliya don fuskantar hukunci don zama ishara ga wasu.

ADVERTISEMENT