Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Hukumar NCC ta bai wa makarantar kididdiga ta tarayya kwamfutoci

Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta
Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta

Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Farfesa Umar Garba Danbatta ya ba da tallafin kwamfutocin tafi da gidanka ga Makarantar Kididdiga ta Tarayya (Federal School of Statistics) da ke garin Manchok A Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

A lokacin da ya ke jawabi a wajen raba kwamfutoci 110 da aka gudanar a dakin taro na makarantar, Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Kudu, Sanata Danjuma Laah, wanda ya nemi tallafin, ya ce hukumar ta bada wannan tallafin ne don daukaka cibiyar da kuma saukaka koyo da koyarwa da ayyukan bincike don samar da isassu kuma kwararrun masana a dukkanin bangarorin gwamnati da na masu zaman kansu a fadin kasar.

ADVERTISEMENT

Dan majalisar, wanda daya daga cikin mataimakansa, Alhaji Suleiman Isa ya wakilta, ya ce hukumar ta bayar da wannan tallafin ne don daukaka darajar makarantar zuwa matakin Jami’a wanda tuni kudurin hakan ya yi nisa a majalisar ta dattawa don mayar da ita Jami’ar Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya (Federal Unibersity of Science and Technology) da jama’ar shiyyoyin Arewa ta Tsakiya da Arewa Maso Yamma za su amfani da ita.

A yayin da yake jawabi, Shugaban Makarantar, Mista Mangbon T. Amos (MFR), ya yaba da wannan yunkurin, inda ya roki sauran sassan gwamnatin tarayya da na Tetfund da ETF da PTF da su taimaka wajen gina dakunan kwana na dalibai maza da na mata da dakunan bincike da gyaran hanyar isa zuwa cikin makarantar don saukaka musu.

ADVERTISEMENT

Haka shi ma da yake nasa jawabin a madadin masarautu uku da ke karamar hukumar ta Kaura da suka hada da Morwa da Takad da Kagoro, Dagaci Soja Yayock ya bayyana farin cikinsa da wannan cigaban da aka samu, tare da yin addu’a da kuma fatan ganin mafarkin daukaka makarantar zuwa matakin Jami’a ya tabbata cikin karamin lokaci.