✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NCC ta sake fasalin tsarin lamba ta kasa

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta bayyana cewa tana sake fasalin tsarin kididdiga lamba ta kasa (NNP)  don tabbatar da  tsarin tarho ya tafi da…

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta bayyana cewa tana sake fasalin tsarin kididdiga lamba ta kasa (NNP)  don tabbatar da  tsarin tarho ya tafi da bukatar da ake da ita ta juyin-juya-halin masana’antun da ake ciki.

Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Dambatta ne ya bayyana haka a ranar Lahadi a yayin baje kolin kimiyyar sadarwa da ta tarho karo na hudu da Cibiyar Cinikayya da Kasuwanci ta Legas ta shirya.

Ya bayyana cewa hukumar na sake fasalin tsarin lambar kasa don bullo da sabuwa wacce za ta magance bukatar lamba ta kasa bisa la’akari da karuwar yawan mutanen kasar nan.

Dambatta wanda Mataimakin Darakta Mai Kula da Harkokin Abokan Hulda, Alhaji Ismaila Adedigba ya wakilta, ya bayyana cewa tsarin kididdiga na da muhimmanci ga harkokin sadarwa da tarho dangane da na’urori da wasu ayyuka. Bunkasa sabuwar kididdigar ya ce za ta taimaka wajen samar da lambobin da za su gamsar da bukatun yawan na’urorin Najeriyar da aka kiyasta sun kai miliyan 500  da kuma kimanin biliyan daya na duniya da za a hada su ta hanyar na’urori  zuwa shekara ta 2050.

Sabon tsarin kididdigar ta NNP za ta bunkasa yadda za a raba dukiyar kasa da bunkasa gasa a tsakanin kamfanonin tarho da soke asarar amfani da lambobi da bunkasa sababbin kirkira da karfafa karuwar bangaren tarho da kara samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin kasa da sauransu.

“Hakika an samu karin sabuwar dama a sararin samaniyyar sadarwar Najeriya kuma akwai bukatar a yi amfani da wannan dama a bangaren tarho. Mutane suna da sha’awar su ga dukkan layukan da suke amfani da su a wuri daya. Abubuwa kamar tsarin magana da data da kananan sakonni da shirye-shiryen talabijin da harkokin banki da makamantansu duk kana samunsu ta wayar hannu. Wannan hadaka tana bukatar an bunkasa ta da yin amfani da tsarin lamba don tattara wadannan harkoki. Saboda haka daga yanzu hukumar tana bunkasawa da fadadawa da tsake tsarin lambobin don tabbatar da ’yan Najeriya sun ci moriyar lamarin. Hakika Najeriya na kan gaba wajen yin amfani da sababbin tsare-tsaren kimiyya da fasaha. Hakan yana samuwa ne da sanya ido sosai na masana’antar sadarwa da Hukumar NCC take yi, kuma shi ya sa hukumar take son hakan ya shiga tsarin juyin-juya-halin masana’antu ya zama wani batu na farin ciki amma akwai bukatar karin dagewa don mu ci gajiyar wadannan sababbin kimiyya don alfanun kasarmu,” inji shi.

Ya bayyana bukatar hada hannu don tallafawa wajen gina karin kayayyakin aiki da za su taimaka wajen kara samar da yanar gizo fiye da yadda yake a yanzu na kashi 33 cikin 100 don bunkasa harkokin sadarwa yadda ake gani a yanzu na juyin-juya-halin masana’antu inda komai ake yin sa a yanar gizo.

Farfesa Dambatta ya ce  hukumar tana yin aiki da kamfanonin kafa kayan aikin sadarwa don tallafa wa kayayyakin aikin kamfanonin sadarwa da karfafa gwiwar masu harkokin tauraron dan Adam don su sanya jari a Najeriya tare da yin aiki  da masu ruwa-da-tsaki don samar da yanayin sanya jarin ga harkokin tarho don bunkasa shi fiye da yadda yake a yanzu na fiye da Dala biliyan 70.