✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NDLEA za ta rika kama masu unguwannin da aka samu gonar wiwi a yankinsu

Kwamandar Hukumar Yaki da Miyagun kwayoyi (NDLEA) a Jihar Oyo, Uwargida Omolade Faboyede, ta ce, daga yanzu hukumar za ta fara kama masu unguwanni da…

Kwamandar Hukumar Yaki da Miyagun kwayoyi (NDLEA) a Jihar Oyo, Uwargida Omolade Faboyede, ta ce, daga yanzu hukumar za ta fara kama masu unguwanni da dagatan da aka samu gonakin da ake noman tabar wiwi a masarautunsu. 

Bayanin haka ya biyo bayan gano wata gona mai girman hekta 16 da ake noman tabar wiwi a cikinta ne da hukumar ta gudanar da aikin barbada fetur tare cinna wuta ga gonar da ke tsakanin kauyukan Anisere da Lagbeja a karamar hukumar Akinyele da ke Jihar Oyo.
Bayan kammala aikin lalata gonar da Kwamandar ta jagoranci jami’an tsaro da ’yan jarida a ranar Alhamis ta makon jiya, Kwamandar ta shaida wa shugabannin al’ummomin yankin cewa, “Kada ku rika bayar da filaye ga mutanenku ko baki suna noman wannan ganye mai lahani ga jama’a.”
Ta ce, saboda matsalar da ake samu na kasa gano mutanen da suke noma wadannan gonaki balle a kama su, “Daga yanzu hukumar NDLEA za ta fara kama shugabannin al’ummomi da masu unguwanni da aka gano gonakin da ake noma tabar wiwi a ciki kuma za a rika gurfanar da su ne gaban kotu idan suka amince da irin wadannan miyagun mutane ba tare da sun hanzarta sanar da jami’an tsaro ba,” inji ta.
Kwamanda Faboyede, ta ce hukumar ta samu labarin gonar ce daga wasu mutanen kirki inda ta hanzarta aikewa da jami’an tsaro kafin su yi wa gonar dirar mikiya. Ta ce, duk da yake ba su kama kowa a gonar ba, sai dai, “Mun yi nasarar lalata duk ganyen da ba a girbe ba, kuma mun samu busasshen ganyen da aka girbe mai nauyin kilo 100 da ake shirin durawa cikin buhuna,” inji ta.
Wasu dattijai biyu masu suna Pa Wahabi Anisere da Mista Azeez Adedeji da suka yi magana da ’yan jarida a madadin al’ummar kauyen Anisere, sun ce, filin da aka gano gonar a ciki mallakar kauyen Lagbeja ne kuma wani mai suna Taiye Oyelakin ne yake noma wannan ganye a gonar.
Shugaban karamar Hukumar Akinyele, Mista Abiola Ambali da wasu mukarrabansa, sun yi wa tawagar NDLEA marhabin da jinjina game da gano gonar da lalata ta.
Mista Ambali ya shaidawa ’yan jarida cewa, ya fara daukar matakin gaugawa na gayyatar dagatai da masu unguwannin kauyukan da aka gano gonar domin tattaunawa a samo hanyar da za a magance aukuwar irin haka a nan gaba.