Da Dumi Dumi

Hukumar NNPC ta saka Naira tiriliyan 1.26 a lalitar gwamnati

Hukumar Albarkatun Mai ta Kasa (NNPC) ta ce ta sanya Naira tiriliyan N1.26 cikin asusun Gwamnatin Tarayya a 2018.

A cikin wata takarda da Hukumar ta fitar a ranar Talatar da ta gabata, ta ce kudin ya zarta wanda ta sanya a cikin kasafin kudi na bara, wanda ya kai Naira tiriliyan 1.22.

Daraktan harkokin kudi na kamfanin, Mista Godwin Okonkwo, wanda ya wakilci Daraktan NNPC, Maikanti Baru, yake fadin haka a gaban Kwamitin Majalisar Dokoki ma su bincike a kan zargin da ake yi wa kamfanin kan kudaden da bai mai da su asusun Gwamnatin Tarayya ba a cikin watan Yulin 2017 zuwa Disambar bara.

Mista Baru ya lissafa wadansu hanyoyi biyu da kamfanin ya bi wajen tura kudaden zuwa asusun Tarayya, ta hanyar hada ka da kamfanoni hakar mai wajen sayar da danyen mai da kuma wanda ake sayar da shi cikin gida.

Ya ce, su na bin hanyar da ta da ce wajen sanya  kudaden hada kar a cikin asusun Tarayya.

ADVERTISEMENT

‘’Shugabancin hukumar ta NNPC yana bin duk wata hanya da ta da ce  da kuma taka-tsan-tsan wajen kashe kudaden hakar mai da gas domin kauracewa irin kuskuren baya.

‘’Halin da harkar mai ke ciki yanzu a kasa, hali ne na nasara ga ci gaban kasa. NNPC tana bin wasu matakai na ta ra kudaden shiga domin ci gaban Kasa kuma tana kaucewa hanyoyin zirarewar kudede,’’ inji Mista Okonkwo.

Ya ce Hukumar tana duba litaffin shigar da kudi zuwa asusun Tarayya lokaci zuwa lokaci domin tabbatar ba mu gadar da bashi ga ’yan Kasa ba.

Kuma yayi watsi da zargin da wasu kwamishinonin kudi suke yiwa kamfanin  na NNPC cewa bai sanya wasu kudade a asusun Tarayya ba cikin shekara 2017 zuwa Disambar 2018, ya ce kamfanin yana bin duk wata hanya ta ka’idar kudi tare da masu ruwa da tsaki.

Mista Baru, ya ce saka jari a harkar iskar gas da fetur tana daukar lokaci ka fin ta kai ga gaci,ya kara da cewa idan NNPC ta ki sanya jarin da ya dace to nan gaba NNPC baza tasamu kudin da za ta raba wa rukunin Gwamnati guda ukkun da mu ke da su ba.

Da a ka tambaye shi ga me da ko NNPC ta sanya kudaden harajin 2018, sai yace a cikin watan gobe hukumar zata fitar da Jadawalin kudaden da ta ta ra kuma ta saka a asusun Tarayya.

Ya ce Hukumar NNPC ta yi bayani a kan duk wata takaddama ta kudaden shekarar 2018 kuma ta yi bayanin abin da ya jawo tsaiko.

Shugaban kwamitin na majalisar, Chukwuka Onyema, ya gode wa kamfanin na NNPC yadda ya amsa gayyatar su kan lokaci.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya