✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NYSC za ta hukunta danta da ya yi magudin zabe a 2019 – Janar Kazaure

Shugaban Hukumar Kula da Masu Hidimar Kasa (NYSC), Janar Sule  Zakari Kazaure ya ce duk wani mai hidimar kasa da ya kuskura ya bari wata…

Shugaban Hukumar Kula da Masu Hidimar Kasa (NYSC), Janar Sule  Zakari Kazaure ya ce duk wani mai hidimar kasa da ya kuskura ya bari wata ko wani dan siyasa ya yi amfani da shi wurin aikata magudin zabe, to ya kuka da kansa, domin Hukumar NYSC za ta tabbatar da cewa an hukunta shi.

Kazaure ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi ga masu yi wa kasa hidima da aka tura Jihar Kebbi kan ayyukan zabe da zasu gudanar a 2019 mai zuwa a sansanin horas da masu yi wa kasa hidima da ke Dakingari a Karamar Hukumar Suru.

An shirya masu taron ne don tabbatar da cewa sun gudanar da ayyukan zaben na shekara ta 2019 mai zuwa cikin gaskiya da adalci ga al’ummar kasar nan baki daya. Inda shugaban ya ce “kada wanda ya yarda wani dan siyasa ya yi amfani da shi wurin canza sakamakon zabe ko satar akwatin zabe yayin gudanar da ayyukan nasu”.

Shugaban Hukumar ta NYSC wanda Mataimakin Darakta a Sashen Gudanarwa ya wakilta, Barde Usman ya jaddada cewa gaskiya da adalci a lokacin da zasu gudanar da ayyukan zaben kasa mai zuwa na da matukar muhimmanci.

Ya ce “nan bada jimawa ba za a turo tawagar mutane daga babban  ofishin hukumar dake Abuja zuwa Kebbi domin horas da ku kan yadda zaku gudanar da ayyukan zaben 2019. Aikin zabe ga masu yi wa kasa hidima ba dole ba ne sai ga mai ra’ayin yin aikin. Saboda haka idan lokacin yin aikin ya yi, ku tabbatar da cewa rayuwar ku tafi duk abin zaku samu,” inji shi.

Haka kuma ya ce masu yi wa kasa hidima dubu 2 da 39 ne aka turo a Jihar Kebbi daga cikinsu akwai mata dubu 1 da 24 wadanda tun sa’adda suka shigo sansanin horaswa, an bayyana musu dokokin yi wa kasa hidima da hukumar ta tanadar. Haka kuma an gaya musu yadda ake yin ladabi da biyayya yayin yi wa kasa hidima.