Da Dumi Dumi

Hukumar Sharia ta horar da mawakan Annabi a Kano

A makon jiya ne Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta shirya bitar yini daya ga mawakan yabon Manzon Allah (SAW) kan yadda za su rika zabar kalmomi lokacin wakokinsu.
Da yake jawabin maraba, Shugaban Hukumar Shari’a ta Jihar Kano Shaikh Sayyadi Bashir Tijjani Usman Z/Bare-bari ya ce bisa ga yadda ake samun kura-kurai a cikin kalmomin mawakan, ya sa hukumar ta shirya musu bita kan yadda za su rika zabar kalmomin da suka dace a danganta su da Manzon Allah (SAW).
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Sani Abdullalhi Tofa Darkatan ya ce daga yanzu hukumar za ta gurfanar da duk wani mawaki da ya ki bin umarnin hukumar, har a yanke masa hukunci.
A mukalar da ya gabatar Limanin Masalalcin Juma’a na Kanzu ya ce: “Akwai bukatar a zabo tare da tantance kalmomin da za a yi wa Ananbi wake da su. Ba kowace kalma da aka saba yabon sauran jama’a za a yi amfani da ita wajen yabon Annabi ba.”
Shugaban kungiyar Inuwar Sa’irai ta Jihar Kano, Malam Shariff Sidi Abba (Hayyakalla) ya ce “Wannan bita za ta samar da hadin kai tsakaninmu mawaka, ba kamar da, da kowa yake kokarin nuna fifikon darikar da yake kai ba. An nuna mana Musulunci shi ne abin da ya kamata mu ba muhimmanci ba wai kowane mawaki idan ya tashi wakensa ya rika yabon darikarsa kawai ba.      
Idan za a iya tunawa kwanan baya Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta kama wani mawakin Annabi (SAW) wanda aka fi sani da Taka lafiya bisa zargin sa da laifin sanya kalaman da ba su kamata ba a cikin wakokinsa inda yake fadin cewa wai Burhama yake bautawa.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya