Da Dumi Dumi

Hukumar Tsabtace Muhalli ta Jihar Katsina ta yi dace

Hukumar Kula da Tsabtace Muhalli ta Jihar Katsina(SEPA) ta yi dacen shugaba. Tun lokacin da Alhaji Isah Sa’idu Barda ya zama Shugaban Hukumar aka samu ci gaba sosai a fannin tsabtace Jihar Katsina. Shigarsa ofis ke da wuya ya fara aiki wurjanjan wajen samar da wurare da kwama-kwamai inda jama’a za su rika zuba shara, sabanin kafin zuwansa inda ake zubar da ita barkatai. Ya kuma samar da wuraren yin ba-haya da wanka a cikin farashi mai sauki. Safe da rana ma’aikatan hukumar suna share titunan birnin jihar gami da yashe magudanun ruwa a kai-a kai.Da fatar jama’a za mu ba shi goyon baya domin ci gaba da wannan kokari da yake yi

Haruna Muhammad Katsina.Shugaban Kungiyar Muryar Jama’a. (07039205659)

 

 

ADVERTISEMENT
Share