Search
Subscribe
Hukumar Zakka ta raba buhun gero 220 da kudi ga mabukata

Hukumar Zakka ta raba buhun gero 220 da kudi ga mabukata

Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato ta raba wa mabukata buhun gero 220 da kudin da yake kimanin dubu 600 a ranar Talata da ta gabata a Jihar Sakkwato.

Shugaban Hukumar, Malam Lawal Maidoki ne ya bayyana hakan a lokacin da yake rabon.

a cewarsa, “a yau ma kamar kullum muna raba kayan tallafin nan ga mabukata faga Gwamnatin Jihar Sakkwato zuwa ga marasa karfi da marasa lafiya.

“Mabukata  200 ne za su amfana da buhun gero 200 da kuma kudi Naira dubu 2 kowannensu domin yin kudin mota. Haka kuma za mu ba masu ciwon sukari 20 buhun alkama daya daya da kudi dubu 10 domin rage musu radadin ciwo.”

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin