Daily Trust Aminiya - Hukunce-hukuncen zabe: Kotuna sun samu ’yanci  a Gwamnatin B
Subscribe

Cif Garba Paul (SAN)

Hukunce-hukuncen zabe: Kotuna sun samu ’yanci  a Gwamnatin Buhari – Garba Paul

Wani Babban Lauyan Najeriya (SAN) da ke zaune a Jos,  fadar Jihar Filato, kuma babban lauyan da ya jagoranci kare zaben Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong,  a Kotun Sauraron Kararakin Zabe da Kotun Daukaka Kara. Cif Garba Poul (SAN) ya ce kotuna sun samu ’yancin kansu, a  zamanin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.                                                                                                                                                  Cif Garba Poul ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos, inda ya ce yanzu kotuna sun samu zaman kansu a karkashin mulkin Shugaban Muhammadu Buhari, ba a tozarta masu kuma  ba a sa su dole, sabanin zamanin gwamnatocin da suka gabata.

Ya ce shi ne ya sa a Jihar Zamfara, duk da  cewa Jam’iyyar APC ce take mulki, amma kotu ta kore su kuma suka hakura, suka bi doka. Saboda Shugaban Kasa Muhammadu  Buhari, ya ce dole a yi biyayya ga kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma  dole ne a bi umarnin kotu.

“Yanzu ba a tozarta kowane alkali a Najeriya, sai dai  alkali ya sanya son zuciyarsa kawai. Amma mulkin Buhari ya bai wa alkalai dama su yi gaskiya tsakaninsu da Allah da dokokin Najeriya,” inji shi.

Da ya juya kan zaben Gwamnan Jihar Filato da ya gabata, Babban Lauyan ya ce  babu laifi don Sanata Jeremia Usaini na Jam’iyyar PDP  ya nemi kujerar Gwamnan Jihar Filato. Ya ce amma mutanen Filato ba su ba shi goyon baya ba. Kanensa Gwamna Lalong na Jam’iyyar APC suka bai wa goyon baya, amma ya ki amincewa ya tafi kotu, manyan alkalai da manyan lauyoyi suka goga shari’a, alkalan suka duba karar suka ce Gwamna Lalong ne  ya ci zaben.

Ya ce da bai gamsu ba, sai ya kara gaba zuwa Kotun Daukaka Kara, manyan alkalan kotun da manyan lauyoyi suka duba nan ma suka ce Lalong ne, ya  ci zabe.

“Koda yake yana da damar ya tafi Kotun Koli, amma ina shawartarsa kan ya nuna dattako,  ya mara wa Gwamna Lalong baya kan kudurin da ya sanya a gaba na kawo zaman lafiya a Jihar Filato.Ya tuna Allah Ya ba shi dama, ya yi Gwamna tun Lalong bai shiga jami’a ba a tsohuwar Jihar Bendel wadda yanzu ta zama jihohin Delta da Edo. Kuma ya yi Ministan Abuja, don haka ya kamata ya gode wa Allah kan wannan dama da Ya ba shi, ya mara wa Gwamna Lalong baya,” inji shi.

Da ya juya kan zaben Gwamnan Jihar Filato na shekarar 2023, Babban Lauyan ya ce duk wani dan Jihar Filato ya san cewa kujerar Gwamnan Jihar, za ta koma yankin Filato ta Tsakiya ne a zaben 2023.

Ya ce lokacin da aka dawo mulkin dimokuradiyya a kasar nan, tsohon Gwamnan Jihar Joshua Dariye daga Filato ta Tsakiya ya yi shekara 8, daga nan tsohon Gwamnan Jihar, Jonah Jang daga Filato ta Arewa ya yi shekara 8, yanzu kuma Gwamna Lalong daga Kudancin Jihar ne ke mulki. Don haka  idan ya gama kujerar Gwamnan za ta koma yankin tsakiyar jihar ne a zaben 2023.

Ya ce don haka ya  zama wajibi sauran yankunan jihar,  su mara wa Filato ta tsakiya a zaben shekarar 2023, domin a fitar da Gwamna nagari da zai jagoranci jihar.

texem
More Stories