✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukuncin kotunan zabe: Wasu na kuka wasu na guda

Hukuncin da kotunan zabe suke yankewa suna sanya wadansu ’yan siyasar kasar murna, da guda yayin da wadansu kuma suke kuka suna cewa za su…

Hukuncin da kotunan zabe suke yankewa suna sanya wadansu ’yan siyasar kasar murna, da guda yayin da wadansu kuma suke kuka suna cewa za su daukaka kara a daidai lokacin da kotunan zaben gwamnoni suka fara kammala ayyukansu a sassan kasar nan.

Tuni dai dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya daukaka kara zuwa Kotun Koli, inda yake kalubalantar hukuncin da Kotun Zaben Shugaban Kasa ta yanke na yin watsi da karar da ya shigar.

A Najeriya zabe abu ne mai matukar tsadar gaske, inda ’yan siyasa ke kashe makudan kudi daga fara neman gurbin tsayawa takara zuwa yakin neman zabe da yin zaben da kuma kashe kudi a shari’a wajen kare nasara ko kalubalantar rashin nasara.

A zaben bana, an fafata zaben Shugaban Kasa da gwamnoni a wasu jihohi da na majalisun dokoki na kasa da na jihohi da kuma kananan hukomomin Babban Birnin Tarayya Abuja. Sai dai bayan zaben, wadanda ba samu nasara ba sun garzaya kotu, inda suke bukatar kotu ta soke zaben, bisa zargin cewa an tafka magudi.

Kotunan zaben sun yanke hukunci a jihohi da dama, inda  wadansu daga cikin wadanda aka zaba suka ci gaba da murnar tabbatar musu da nasararsu da kotunan suka yi, yayin da wadansu kuma suke kuka kan hukuncin.

Akalla jam’iyyu 90 ne suka fafata a zaben gwamnonin na bana da aka yi ranar 9 ga watan Maris.

A Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i na Jam’iyyar APC ne ya doke dan takarar Jam’iyyar PDP Isah Ashiru da kuri’a miliyan 1, da dubu 44da 710, Ashiru kuma ya samu dubu 814 da 168.

Bayan sanar da sakamakon zaben, Isah Ashiru da Jam’iyyar PDP sun shigar da kara a Kotun Zabe ta Jihar Kaduna, inda suka bukaci a soke zaben, amma Shugaban Kotun, Mai shari’a Ibrahim Bako ya kori karar, tare da tabbatar da Nasir El-Rufa’i a matsayin zababben Gwamna a ranar 9 ga Satumban nan.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Kaduna Hassan Hyat ya nuna shirinsu na daukaka kara, inda Mataimakin Daraktan yakin zaben Isah Ashiru, Yakubu Lere ya tabbatar da cewa za su daukaka kara.

A Jihar Kano, har yanzu ana sauraron hukuncin kotun zaben, a shari’ar da ke gudana a tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jam’iyyar APC da Abba Yusuf na Jam’iyyar PDP. Ganduje ne ya lashe zaben, Abba ya kai kara kotu.

A Jihar Katsina kuwa, Kotun Zaben ta tabbatar da zaben Gwamna Aminu Bello Masari, duk da cewa an samu hukunci biyu a shara’ar, inda Mai shari’a E.B. Omotoso da A.I. Ityonyiman suka tabbatar da zaben, ita kuma Mai shari’a Hadiza Ali Jos ta soke zaben.

Da yake yanke hukuncin masu rinjaye, Mai shari’a Ityonyiman ya tabbatar da zaben Aminu Bello Masari. Tuni Sanata Yakubu Lado da Jam’iyyar PDP suka nuna shirinsu na daukaka kara.

Ana sauraron hukuncin Jihar Sakkwato, inda Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya doke dan takarar Jam’iyyar APC, Ahmad Aliyu na APC.

A Jihar Neja, kotu ta tabbatar da zaben Abubakar Sani Bello, inda kuma dan takarar PDP, Umar Nasko ya ce za su daukaka kara. Babban lauyan PDP, Mohammed Ndayako ya ce ba za su amince da hukuncin kotun ba, inda ya ce za su daukaka kara.

A Jihar Kuros Riba, dan takarar APC Sanata John Owan-Enoh da ke kalubalantar zaben Gwamnan jihar Ben Ayade ya ce zai daukaka kara kan hukuncin Kotun Zaben.

A Jihar Ogun, dan takarar Jam’iyyar APM, Adekunle Akinlade ya ce zai daukaka kara bayan Kotun Zaben ta kori karar da ya shigar, inda yake kalubalantar zaben nasarar Gwamna Dapo Abiodun na APC.

A Jihar Gombe kuma, masu kalubalantar zaben Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya guda uku tun a watan Afrilu suka janye kararsu.

A Jihar Taraba, Kotun Zaben ta tabbatar da zaben Gwamna Darius Ishaku na Jam’iyyar PDP ne, bayan ta yi watsi da karar dan takarar Jam’iyyar APC, Abubakar Danladi.

Sai Jihar Imo, Kotun Zaben ta tabbatar da zaben Mista Okezie Ikpeazu na Jam’iyyar PDP, bayan ta yi watsi da karar da dan takarar babbar jam’iyyar adawa a jihar ta APGA, Dokta Aled Otti ya shigar.

A Akwa Ibom ma  Gwamna Udom Emmanuel na Jam’iyyar PDP da ya lashe zaben ne, Kotun Zaben ta tabbatar da nasararsa.