✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibrahimobic ya sabunta kwantaraginsa a kulob din PSG

Shahararren dan kwallon kulob din Paris Saint Germain  PSG da ke Faransa, Zlatan Ibrahimobic ya sabunta kwantaragin shekara daya a kulob din.  dan kwallon ya…

Shahararren dan kwallon kulob din Paris Saint Germain  PSG da ke Faransa, Zlatan Ibrahimobic ya sabunta kwantaragin shekara daya a kulob din.  
dan kwallon ya bayyana cewa ya yanke shawarar sabunta kwantaraginsa ne bayan yardar da ya yi a halin yanzu babu wani kulob da yake kauna da ya fi na PSG a duk fadin duniya.
Kodayake ejent din dan kwallon mai suna Mino Raiola ya nemi a sabunta masa kwantaragin shekara uku ne, amma hakan ba ta yiwu ba, shekara daya kawai aka karawa dan kwallon.
Ibrahimobic, dan kimanin shekara 31, ya taba buga kwallo a kulob din FC Barcelona da ke Sifen kafin ya canza sheka zuwa AC Milan da ke Italiya daga bisani ya koma Faransa inda ya cigaba da yin kwallo a kulob din PSG.