Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

ICPC za ta hukunta ’yan siyasar da ke karkatar da kudin aikin mazabu

ICPC logo

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da ta Kasa (ICPC) ta sha alwashin hukunta duk wani dan siyasa ko dan kwangilar da aka ba shi kudi don gudanar da aiki a mazabarsa amma ya karkatar da kudin ba tare da dalili ba.

Shugaban Hukumar ICPC Mista Bolaji Owasanoye ne ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba a Abuja, lokacin da yake kaddamar da ayarin da hukumar ta samar don bin diddigin yadda ake gudanar da ayyuka a kowace mazaba a fadin kasar nan (CPTG).

ADVERTISEMENT

Binciken da Aminiya ta yi, ya gano cewa tun da aka fara ba ’yan siyasa kudin da za su rika yin aiki a mazabunsu fiye da shekara 10 da suka wuce, ana kashe kimanin Naira biliyan 100 a kowace shekara kan haka.

Mista Owasanoye ya kara da cewa ganin yadda ake ware wa ’yan siyasa kudi a kowace shekara don gudanar da ayyuka a mazabunsu amma suke karkatar da kudin abin akwai tashin hankali. Wannan ya nuna suna karkatar da kudin ne kawai maimakon yi wa al’umma aiki.

ADVERTISEMENT

Ya ce alal misali, binciken da hukumarsa ta yi a shekarar 2015 a jihohi 16 game da ayyuka 436 da aka ce an bayar, ta gano ayyuka 145 ne kacal aka kammala yayin da ba a kammala ayyuka 77 ba sannan ba a aiwatar da komai a kan ayyuka 211 da aka ce an bayar da kwangilarsu ba.

 Shugaban Hukumar ICPC Bolaji Owasanoye

Ya ce haka abin yake a shekarar 2016, inda binciken da hukumarsa ta yi ya gano an bayar da ayyuka 852 a jihohi 20 amma 350 daga cikinsu ne kadai aka kammala yayin da ake ci gaba da aiki a wasu 118 sannan ba a tantance ayyuka 41 da aka ce an bayar a wasu mazabu ba, yayin da kuma ba a aiwatar da komai a ayyuka 350 ba, wanda hakan ke nuna an karkatar da irin wadannan kudade ne.

Ya ce a kan haka ne Hukumar ICPC za ta fara sanya ido daga yanzu don ganin an hukunta duk dan siyasa ko dan kwangilar da aka ba aiki amma ya karkatar da kudin bai yi ba.