Da Dumi Dumi

Idan aka bai wa manomi taki da jari za a sha mamaki – Sanyinna

Alhaji Abubakar Sadik Sanyinna, sanannen manomi ne da ya shahara a noman gero da masara da wake da auduga da kuma ridi da sauransu. Shugaba ne a kungiyoyin manoma daban-daban a nan Najeriya. Aminiya ta zanta da shi kan daminar bana da abubuwan da suka shafi noman a kasar nan.

 

Aminiya: Me zaka ce kan daminar bana a kasa baki daya?

Sanyinna: Sai godiyar Allah da ya nuna mana daminar bana da aka dade ba a samu irinta mai albarka ba, ta yi kyau ko wanda bai san noma ba ya san an samu abinci a bana, Allah Ya taimaka an samu amfanin gona mai kyau, tun a farko damina ta zo da ruwa da rana abin da shuka ke so, wannan alamar samun amfani kenan kuma an samu. Manoma na cikin godiyar Allah an samu daminar da an dade ba a samu irinta ga amfanin gona ba, duk abin da aka shuka ya yi kyau a wannan shekara, an dade ba a samu shekarar da duk amfanin gonar da aka shuka ya yi kyau kamar wannan shekarar ta bana ba. 

ADVERTISEMENT

Aminiya: Me kake ganin ya sanya al’ummar Najeriya musamman na Arewa rungumar noma gadan-gadan 

Sanyinna: Abin da ya jawo haka shi ne rashi da matsi, don shi ke sanya a kirkira wani abu da zai kawo maslaha, a bara mutane sun ga an samu hauhawar farashin abinci ba kudi, jarabawa ce da kasar ta fada ciki a bara ne aka shiga matsin, a bana sai kowa ya matsa kaimi a noman in kana noma hekta biyar ka koma goma in baka zuba taki a gona ka canja salo don noma ba ta ki juya kasa ne kawai, wadanda suka bar noman saboda wahalar da ke ciki ba wani amfani da riba babba sun dawo saboda akwai riba yanzu ta kudi da ciyar da gida, in baka noman ka fara yi yanzu sai aka hada karfe da karfi sai abu ya yi yawa don an samu kari da alamu kuma sauki ya zo.

Aminiya: Wadanne abubuwa ne kake ganin ya kamata gwamnati ta yi don kara habaka harkar noma a kasar nan?

Sanyinna: To matsalar da ake samu da za a ce gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi suna son taimakawa manoma da gaskiya ba magana ta siyasa ba, to ba wani abu da ya kamata a baiwa karfi da ya kai noma, duk cikin abin da ake yi a duniya ba abin da ya fi noma. Domin duk kasar da ba ta iya ciyar da kanta da abinci ba ta yi nasara ba, duk kasar da sai ta yi bara ga wata kasa a kawo mata abinci to ta fadi, ya kamata ku iya noma abincinku har ku sayar don samun lada da la’ada, don duk wanda ya yi hanyar ciyar da wani bai fadi ba, don albarkar dake cikinsa, ga rage yawan zaune gari banza. Gwamnati ta fito ta taimakawa manoma da karfinta don kara habaka arzikin kasa, ba wani abu da ake kira noma sai jari (kudi) a baiwa manomi taki da kudi za a sha mamaki, in dai da gaske gwamnati ke yi ta taimakawa manomin gaskiya don ciyar da kasa da abinci.

Aminiya: Ya kake kallon aikin kwamitin da gwamnatin Jihar Sakkwato ta kafa don farfado da aiki noma a jihar?

Sanyinna: Gaskiya kafa kwamitin farfado da aikin noma a jihar Sakkwato mutane sun yi marhabin da jin dadin matakin gwamnati. Mai Alfarma Sarkin Musulmi da dukkan sarakunan jihar da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar noma sun halarci taron kaddamar da kwamitin, amma kash wannan kwamitin sama da shekara biyu da kafa shi kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, domin ba wani abu da manomi zai ce an yi masa ta wannan kwamitin don habaka harkar noma a Jihar Sakkwato, kwamitin ya fito da tsarin rabon alkama ya baiwa wasu manoman da shi ya gamsu da su, amma ya ba su alkama maras kyau da injin ban ruwa ba taki ba kudi suka fara aikin na alkama, suka zo tsakiya da yawansu suka jefar da noman don ba kudin da mutum zai sayi man da zai sanyawa injin ya yi ban ruwan alkamar, kashi 60 cikin 100 na wadanda aka baiwa hakan ya same su, wadanda kuma suka tsaya har alkamar ta girma ba kwaya, don da ma can ba mai kyau ce, tsawon wahalar da suka sha haki ne suka rena har ya girma aka girbe ba a ba su komai ba. 

Kwamitin ya sake kawo irin shinkafa ya ce duk wanda ya baiwa zai ba shi taki buhu shida a hekta, amma aka zo ana baiwa mutane taki buhu daya kuma ba ko naira daya na tallafi ko bashi, a hakan manoman suka cire shinkafa ba wani tallafi da aka ba su, mafi yawan manoman da ke cikin shirin ba su dogara da kwamitin ba, hakan ya sanya ba mai jiransu a duk lokacin da suka yi magana, ji ne kawai dole, a kwanan nan ne aka ce an fara ba da tallafin amma an dakatar don wai an samu ana canja wasu da wasu, ka dubi duk wahalar nan da mutane ke yi fa an sanya su buda asusun ajiya da za a turo masu kudin bashin noma da wasu abubuwan tantancewa, sun yi ta yawo ko wannan takin zamani an kasa ba su, zaka samu a mazaba an ba da buhun taki 10 ko rabin kwano aka yi wani manomi ba zai samu ba.   

Idan ka duba duk wadannan gwamnati ce kawai ke fadin tana wani abu a harkar noma, ko ba da gaskiya take fadin haka ba ko ba ta son abin ya yi tasiri, duk da manoma suna son sana’arsu, ina kira ga gwamnati in ta tsara abu da kyau to ta aiwatar, ta shigo da malaman gona don ba da shawara da gayawa manoma irin da za su rika amfani da shi, matsawar ba malaman gona tare da manomi, to akwai cikas ga harkar noman, a dubi nasarorin da noma ke samu a jingine siyasa a harkar noma a taimakawa manoman gaskiya ba dalilin da zai sanya a shigo da siyasa a harkar noma in har ana son bunkasa aikin noma a wadatar da kasa da abinci.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya