✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan Buhari ya bar APC ba za ta kai wata uku ba – Gwamna Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce Jam’iyyar APC ba ta da karsashin da za ta kai gaci a fagen siyasar kasar nan, kuma…

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce Jam’iyyar APC ba ta da karsashin da za ta kai gaci a fagen siyasar kasar nan, kuma ’yan Najeriya ba za su yi kuskuren mika mata ragamar mulkin kasar nan ba.  Gwamnan ya fadi haka ne a lokacin da shugabannin kungiyar Editoci ta kasa suka kai masa ziyarar girmamawa a gidan gwamnati da ke Dutse, inda ya ce Jam’iyyar APC jam’iyyace da ba ta da wani kwarjini ko tagomashi in aka dauke Janar Buhari, kuma idan Janar Buhari ya bar ta ba za ta yi wata uku ba za ta mutu. Alhaji Sule Lamido ya ce APC jam’iyyace da aka kafata domin wata manufa ta daban, kuma hadaka ce ta mutanen da suke da wani nukufurci a cikin zukatansu. “Mafi yawan wadanda suke cikin Jam’iyyar APC mutane ne da aka bata masu ta hana su tsayawa takara a wasu jam’iyyu suka koma APC da nufin biyan bukatar siyasa,” inji shi. Ya kara da cewa galibin wadanda suke surutu a yau a APC ba su isa su yi magana ba a 1998 saboda matsorata ne “amma mu a lokacin ne muka tsaya muka kafa Jam’iyyar PDP wadda ta dawo da martabar ’yan kasa da mutuncin al’umma a yau suka samu damar zaginmu. Mu ne muka mayar da shugabanci ya zama karba-karba saboda muna son su ma Yarbawa a dama da su a shugabanci lamarin da ya ba Obasanjo damar shugabantar kasar nan duk da jama’a ba sa sonsa,” inji shi.