Da Dumi Dumi

Idan kun isa ku fice daga PDP – Sanata Gada ga Gwamnoni 7

Sanata Abubakar Umar GadaSanata Abubakar Umar Gada shi ne mai ba Shugaban Jam’iyyar PDP a kasa Alhaji Bamanga Tukur shawara kan harkokin siyasa, tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a Jam’iyyar PDP kuma daya daga cikin mutanen da ke takun-saka da Gwamna Wamakko a zantawarsa da wakilinmu ya kalubalnci gwamnonin nan bakwai da suka yi ‘tawaye’ su fice daga jam’iyyar in suna jin suna da farin jini a wurin jama’arsu:

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Aminiya: Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yi zargin cewa wadansu ’yan siyasa ’yan asalin jihar mazauna Abuja suna zame mata kafa, kuma muzahararar da ’yan Shi’a suka yi wani yunkuri ne na neman hargitsa jihar tare da sanya hannun wani dan siyasa dan asalin jihar da ke Abuja, me za ka ce kan haka?
Sanata Gada: Wadannan kananan maganganu shaci-fadi ne kawai. Sun firgita ne ganin yadda mutane ke Allah tsine ga gwamnatinsu saboda ta’addancin da suka jima suna aikatawa. Da mamaki kawo siyasa cikin abin da ya auku wanda kowa ya san cewa ba harkar siyasa ba ce. Mutanen Jihar Sakkwato sun gaji da halin kuncin da gwamnatin Wamakko ta sanya su ciki saboda haka suke neman canji. Amma dangane da amsar tambayarka, ni dai kowa ya san ba dan Shi’a nake ba. Ina adawa da Shi’a saboda rashin gamsuwa da yadda suke tafiyar da harkokin addininsu. Wannan shi ne akidata game da Shi’a kuma abin da na yi imani da shi ke nan. A bangaren gwmnati, mene ne gamin ’yan Shi’a da Gwamnatin Tarayya? Mene ne dangantakar Shi’a da Gwamnatin Tarayya? Hakkin wane ne wanzar da zaman lafiya da kare doka da oda? Mu a bangaren jam’iyya hakkinmu ne mu kare dokokin jam’iyya kuma a saisaita hankalin wanda ya ki bin dokokin jam’iyya. Duk wani mutum da ya san yana da matsala da jam’iyya to ya fadi, sai dai in ba ka da abin fadi, shi ke nan. Na fadi, wadannan mutane da aka saki an sake su ne bisa umarnin kotun Jihar Sakkwato ba kotun Tarayya ba, to ta yaya kotun jiha za a ce Gwamnatin Tarayya za ta gudanar da ita? Idan kotun jiha ta sake su ina ruwanmu? Ni ban ma san ko daya daga cikin mutanen da aka sako ba, wannan ba ma wani lamari ne da ya kamata a rika magana kansa ba, don ya shafi addini, mu dai mana son a samu zaman lafiya a jam’iyyarmu, muna da matakan ladabtar da duk wanda ya saba wa dokar jam’iyyarmu.
Aminiya: Akwai jita-jitar da ake bazawa a gari wai kana kokarin karbe kujerar Minista na Jihar Sakkwato?
Sanata Gada: Shin ina bukatar zamowa Minista domin tallafa wa jama’ata, ko ina son kujerar don ra’ayi na siyasa kawai? Koko dai ina muradin Ministan saboda yin siyasa ta ayyukana kawai?  Wannan shaci-fadi ne na mutane kawai. Mutane na amfani da bahaguwar fahimta inda suke fadin duk abin da suke hasashe, sai dai lokaci na tafe da jama’ar da ke wannan zargi za su gane bambanci tsakanin gero da tsakuwa.
Aminiya: Jam’iyyarku ta tsunduma cikin rudani, alhali zaben shekarar 2015 na karatowa mutane da dama na ganin al’amarin zai iya karan-tsaye ga yukurinta na samun nasara, mene ne ra’ayinka game da haka?
Sanata Gada: Wannan rudani ba zai yi mana cikas ba ta ko’ina don jam’iyyar ta nasara ce. Idan wadannan gwamnoni guda bakwai sun ce suna da farin jini, to, su canja sheka su gani, ko akwai wasu mutane da za su bi su kamar yadda suke fadin su ake yi ba jam’iyya ba. Su gwada komawa wata jam’iyya su gani mutanen za su bi su sai duniya ta gani. Jam’iyyar da ta taimake ka ta sanya ka cikin muhimman mutane a siyasa da gwamnati kuma ita ce za ka yi tunanin juya mutanenta yadda ka ga dama? To ka fita waje ka ga yadda rayuwa take. Na kalubalance su da su bar PDP, in har ba su iya bin dokoki da ka’idojin jam’iyyar. Idan har ba za su yi tunani mai kyau ba da zai hana wa jam’iyyar shiga cikin kangi, na kalubalance su da su bar jam’iyyar kila a samu masu bin su.
Aminiya: Suna zargi shugaban Jam’iyyar PDP na kasa da yin uwa da makarbiya kan rikicin me za ka ce?
Sanata Gada: Mene ne Bamanga Tukur ya yi da ya saba wa doka? Mene ne ya aikata wanda ba daidai ba? Ya kamata su gaya mana laifi daya tak da ya aikata. Koda wani ya fito ya ce Bamanga Tukur ya saba wa tsarin mulkin jam’iyya ko kasa, to karya zai yi kowa ya san haka. Ina kira ga jama’a su yi bayani ta yadda zai gyara jam’iyya ko wani kuskure da aka yi a shirye shugaba yake ya ba da hakuri, ba wai mutum ya zo don yana da wani nufi a zuciyarsa ya karkatar da tunanain mutane ba, ba za mu yarda da haka ba.
Aminiya: Akwai jayayya da mutane ke yi kan taron kasa da ake son a gabatar menen e ra’ayinka?
Sanata Gada: kasar nan tana kunshe da kabilu da addinai mabambata, akwai bukatar magana daya da za a samar don kowa ya girmama dan uwan zamansa. karshen zaman za a fito da matsalolinmu ga ’yan kasa a ba da damar kowa ya fadi yadda yake ganin ya dace a gyara domin samun ci gaban kasarmu. Ya kamata mu fahimta da kyau kan tsarin dokokin kasar nan don samun matsaya da ra’ayi daidaitacce. A jiye son kai wanda shi ne zai ba ’yan majalisarmu kwarin gwiwar gabatar da wannan dokar. Wannan tunani ne mai kyau da zai taimaki kasar nan a samu ci gaba, wasu abubuwa da kake gani rashin fahimta ne wasu kuma rashin kulawa, wasu rashin samun cikakken bayani ne da fadakarwa. Duk wadannan abubuwa an san da su kuma za a magance su lokacin tattaunawar. Bayan wannan mutane za su ji dadi ganin rage ratar da suke da ita a gundumominsu da yankunansu da addininsu, za su ga ana tafiya bai-daya don ci gaban kasa.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya