✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idon makaho ya dawo bayan shekara 21

Wani matashi mai shekara 24 mai suna Edmond Eli da ya kwashe shekara 21 yana fama da makanta ganinsa ya dawo. Yanzu haka Edmond ya…

Wani matashi mai shekara 24 mai suna Edmond Eli da ya kwashe shekara 21 yana fama da makanta ganinsa ya dawo.

Yanzu haka Edmond ya kammala shirin komawa makaranta domin ci gaba da neman ilimi bayan ya warke garau.

Kafar Legit ta ruwaito cewa Eli ya gamu da cutar makanta ce bayan shekara 3 da haihuwarsa, wanda haka ya yi ta fama da ita har zuwa karshen makon jiya inda ya yi gamo-da-katar da wani aikin ido kyauta da Sanata Binos Yaroe na Jihar Adamawa ya dauki nauyi a Karamar Hukumar Demsa.

Da yake zantawa da manema labarai, mahaifin Eli ya ce cutar makantar da dansa ya yi fama da ita a baya ta sanya ba ya zuwa makaranta, kuma ya zamo bayan yawan magana da suke yi, ba ya da walwala ko kadan, har sai yanzu da Allah Ya kawo masa sauki.

“Ina mika godiya ga Allah sannan da Sanata Binos tare da likitocin da suka taimaka wajen bude idanun dana Eli. Shirin da nake yi masa shi ne zai koma makaranta don yin yaki da jahilci da zarar ya warke sarai,” inji shi.

Mahaifin ya ce matsalar Eli ta faru ne sakamakon wadansu yara da suka zuba masa kasa a ido lokacin da suke wasan kasa. Sai suka kai shi Babban Asibitin Numan daga nan aka tura su Kano, amma ba su da damar zuwa ba saboda rashin kudi.

Da yake jawabi, Shugaban Likitocin da suka yi aikin, Dokta Ugochukwu Anunwa ya ce kwararrun likitoci ne suka gudanar da tiyata ga Eli bayan sun gano matsalar idanunsa, da ake kira ‘Jubenile cataract’, wato yana. Likitan ya ce kimanin mutum 200 suka cire wa wannan cuta a idanunsu.

A karshe Sanata Binos ya bayyana farin cikinsa da wannan nasara da aka samu ta dawo wa Eli da sauran marasa lafiya ganinsu, kuma ya yi alkawarin ci gaba da irin wannan aikin alheri.