Da Dumi Dumi

Ighalo zai buga wa Man U. a wasanta da Chelsea ranar Litinin – Ole Gunnar Solskjaer

Odion Ighalo bai je wasannin atisaye da Man. United ta yi a Spain ba, sakamakon tsoron cutar Kurona dalilin da aka hana shi takardar izinin shiga kasar.

Dan kwallon Najeriyar, mai shekara 30 ya koma Old Trafford da taka leda ne a matsayin aro daga Shanghai Shenhua ranar 31 ga watan Janairu.

Ighalo ya bayyana cewa sai da ya  rage albashi don ya koma Kungiyar  Manchester United.

Tsohon dan kwallon Watford ya koma buga gasar China a 2017, inda ya fara da kungiyar Changchun Yatai.

Bayan da ya buga kaka biyu sai ya koma Shanghai Shenhua wadda ya buga wa wasa 19 ya kuma ci kwallo 10. Ighalo ya taka rawar gani a gasar cin Kofin Nahiyar Afirka da aka yi a Masar, inda ya ci kwallo bakwai, kuma ya zura biyar a wasannin neman gurbin shiga gasar.

ADVERTISEMENT

Rabon da Ighalo ya buga kwallo tun 6 ga Disamban bara lokacin da ya canji dan wasa a karawar da Shanghai Shenhua ta doke Shandong Luneng 3-0 a gasar FA Cup ta China.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya