✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ighalo zai yi jinyar wata 2

Rahotanni sun nuna cewa xan kwallon Super Eagles na Najeriya, Odion Ighalo ya ji rauni a cinya inda ake ji zai shafe akalla wata biyu…

Rahotanni sun nuna cewa xan kwallon Super Eagles na Najeriya, Odion Ighalo ya ji rauni a cinya inda ake ji zai shafe akalla wata biyu ba tare da ya buga kwallo ba.

Ighalo ya samu raunin ne a wasan da Najeriya ta lallasa Tunisiya da ci xaya mai ban haushi na neman gurbi na uku a Gasar Cin Kofin Afirka da aka kammala a Masar.

Odion Ighalo mai shekara 30 shi ya zura kwallo xayan a raga, wanda hakan ya sa ya zura kwallaye biyar a raga kuma ya zama xan kwallon da ya fi zura kwallaye a gasar, inda ya karvi kyautar Takalmin Zinare.

A daidai minti na 44 ne aka canja xan kwallon a yayin wasan.  Sai dai a ranar Talatar da ta wuce ce likitoci suka tabbatar cewa zai shafe akalla wata biyu ba ya buga kwallo.

Kulob xin sa na Shanghai Shehua da ke Sin bai ji daxin raunin da Ighalo ya ji ba, ganin ana gab da a fara kakar wasa ta bana.

Ighalo dai ya yi murabus daga yi wa Najeriya kwallo jim kaxan bayan an kammala Gasar Cin Kofin Afirka ta bana a Masar.