✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Illa ce mace ta zauna ba ta da sana’a – Hajiya Farida Abubakar

Takaitaccen tarihina Sunana Hajiya Farida Abubakar, ni ’yar asalin Jihar Katsina ce amma an haife ni ne a Kaduna a 1982. Na yi makarantar firamare…

Takaitaccen tarihina

Sunana Hajiya Farida Abubakar, ni ’yar asalin Jihar Katsina ce amma an haife ni ne a Kaduna a 1982. Na yi makarantar firamare a L.E.A Jabi a Abuja, sannan na tafi Kwalejin ’Yan mata ta Bakori, Jihar Katsina wato FGGC Bakori daga 1993 zuwa 1998. Sai na dawo Jami’ar Abuja, inda na yi Diploma. Da na kammala sai na yi aure, daga baya kuma na sake komawa makaranta, inda nake karanta Harkokin Kasuwanci da Sana’o’i a Jami’ar Karatu Daga Gida ta Najeriya wato National Open Unibersity.

Yadda na fara wannan kamfani na burodi

Na fara wannan gidan burodi bayan mun rabu da mijina ina zaune a gida. Sai mahaifina ya kira ni ya ce me zai hana ki fara wata sana’ a? Amma sai ya ba ni zabin cewa idan makaranta nake son komawa in ci gaba da karatu, to babu laifi, shi dai zaman ne haka nan bai so. Sai na fara tunanin me ya kamata in fara, a karshe dai na zabi in fara karatu. Na samu gurbin karatu a Jami’ar  Open Unibersity a Abuja na fara karatu. Ba a jima ba kuma na nemi shawarar kannena a kan sana’ar da zan fara kasancewar makarantar ba takura ni za ta yi ba. Sai suka ce suna ganin zai fi kyau in fara sana’ar burodi. Sai na je na samu mahaifinmu na ce ga abin da nake son farawa, sai ya ce in je in bincika in gaya masa yanayin kayan aikin zuwa injin da sauransu in sanar da shi yawan kudin. To da na bincika sai na ga ya fi sauki a Legas. Sai na tura wa wata kanwata da ke can kudin ta saya ta aiko mini. Ka ji yadda na fara! Koda yake wannan ba shi ne na farko ba. Na taba sana’ar sayar da takalma, amma abin bai yi nisa ba ya lalace.

Me ya sa?

To ka san jarinmu na mata, wani lokacin kana sana’ar kana ci a ciki, kafin ka ankara sai ka ga ashe ka cinye jarin ba ka sani ba. Na sake shiga kasuwancin atamfofi, shi din ma dai babu bambanci da wancan na farkon. To amma cikin yardar Allah ga shi wannan kasuwancin na yin burodi ya fara dorewa.

Nasarorin da na samu da kuma yawan ma’aikatana

Ina da ma’aikata hudu, kuma alhamdulillah, zan iya cewa tun da muka fara wannan kamfani ba mu samu wata cikas da ta sa muka tsaya ba. Domin burodin ya samu karbuwa, mutane suna bukatarsa sosai, kuma duk lokacin da muka yi shi ba ya kwana har ma rige-rige ake yi ana nemansa kafin ya kare. Kuma abin da zai ba ka mamaki shi ne yadda ni da kaina nake raba wannan burodi a motata kullum da safe, domin karfe shida ko shida da rabi na safe nake fita daga gida. A dalilin wannan kwazo da nake yi burodin ya samu karbuwa ainun, har ma ya kasance idan an samu jinkiri ba a kai ba za ka ga mutane suna ta bugo waya suna tambaya. Sannan kuma ana zuwa har nan ana saya sosai.

Abin da ya sa nake kai wa mutane maimakon su zo nan su saya?

Da haka na tallata shi, kuma abin da ya sa har yanzu nake kaiwa shi ne galibi wurare ne na kasuwanci, mafi yawan masu yin sana’ar shayi ko kantuna, inda abokan cinikinsu ke son burodin, sannan kuma galibi ba su da lokacin barin wurin kasuwancin nasu a koyaushe.

Lokacin da na fara wannan burodi  da sunan kamfanin

Shekara guda ke nan da farawa kuma sunan kamfanin burodin shi ne 99J Bakery.

Abin da sunan ke nufi

Wato wannan 99J inkiyar mahaifinmu ce ko kuma in ce maka lambar motarsa ce. To ma’anar J din shi ne Jikamshi a Katsina ke nan, kuma yawanci haka abokansa suke kiransa.

kalubale

To gaskiya kalubale akwai shi, yanzu haka maganar da muke da kai ba mu da wutar lantarki. Ka ga ke nan dole sai da jannareta, don haka tilas mutum ya sayi janareta don gudanar da harkokinsa domin ba za a dogara da kamfanonin lantarki ba. Sannan abu na biyu shi ne man dizel da za a rika zuba wa injunan koyaushe. To ka ga idan ba sa’a ba, sai ribar ta rika shiga uwar kudin a hankali. To amma yanzu abin da muke kokarin yi shi ne kara ma’aikata, mu kara hannu wajen fadada kamfanin.

Abubuwan da ake bukata wajen hada burodi

Abu ne mai sauki, abubuwan da ake bukata wajen hada burodi su ne; fulawa da butter da kwai da sukari da madara da yeast.

Yadda na samu kwarewa wajen koyar da mata sana’o’i ta gidan Rediyon bision FM a Abuja

Ta hanyar karance-karance, kodayake ba fannin da na karanta ke nan a jami’a ba. Amma kasancewata mai son yawan karance-karancen littattafai, ina son sanin ilimin abubuwa da sana’o’i har ma da tarihi. Sannan ina sha’awar kallon shirye-shiryen talabijin a kan abubuwan fasaha da sauransu na Turanci. To a dalilin haka na lakanci abubuwa da dama. Sannan ina da kanne masu yin san’o’in abinci da gugguru  da sauransu. Nakan zauna da su in ji yadda suke yi da kuma irin ribar da suke samu. Haka ’yan uwa ko abokai da suke yin wata sana’a nakan rika tambayarsu. To gaskiya ni mutum ce mai yawan son tambaya a kan abin da na ga ya ba ni sha’awa koda kuwa ba ni da burin yin wannan sana’a. Saboda shi kansa iyawan jari ne.

Abin da ya sa na zabi wannan sana’a ta burodi?

Dalilin kawai shi ne, burodi abinci ne da a kullum ake cin sa, yanzu da wuya ka je gidaje ka ga ana soya dankali da safe, saboda tsadar rayuwa, amma shi burodin Naira 100 in ka saya ka hada da shayi zai kosar da kai, haka iyali a cikin gida ko kuma masu yin shayi a waje. Kai idan ma ta kure wa mutum ko da ruwa zai hada ya ci abin sa. To da ka fara sai ka ga mutane suna so wadansu kuma suna zuwa har inda kake suna saya, musamman ma idan kana yin mai inganci. To wannan shi ya ba ni sha’awa na zabi wannan, amma ba shi kadai ba, wani lokaci muna hadawa da samosa da kek da sauran nau’ukan abinci. Misali idan mutum yana biki ya ce a yi masa abinci, muna yi, muna da mutanenmu a kasa, iyakaci kawai da an ce mana ana bukata shi ke nan sai mu yi maka iya bukatarka. Sannan muna ba da hayar kayayyakin da ake yin abinci idan ana bukata.

Yadda nake kallon shirye-shirye da Gwamnatin Tarayya da na jihohi ke yi don koya wa jama’a sana’o’in dogaro da kai

Hakika abu ne mai kyau. Sai dai kawai wasu lokutan ana samun matsaloli da yawa cikin shirin. Misali idan ka duba za ka ga cewa ba a tallata shirin sosai ta yadda macen da ke cikin gida za ta sani, idan ba tana jin rediyo ba ne shi ke nan ba za ta san me ake yi ba. To sanarwar hatta a rediyon tana yin karanci, ballantana ka yi maganar talabijin, ka ga sai tana da wutar lantarki. To ka ga ke nan har yanzu hanyoyin sanarwar sun yi kadan. A maimakon haka sai ka ga shirin yana kara wa masu karfi, karfi ne kawai. Domin wani lokacin wadanda ke da gata ake koya wa sana’o’in maimakon matan da ke fama da talauci na hakika. Wasu lokutan ma jami’an da ke gudanar da shirin ne za su rika sanya nasu, a karshe sai ka ga shirin da aka yi don talaka ko matan da mazansu suka mutu suka bari da marayu ba su amfana ba.

Kirana ga matan da aka koyar da su da wadanda suke son fara sana’a a karan kansu

Gaskiya ya kamata mata su farka, yanzu maganar da ake ta yi kullum a kan matan da mazansu suka mutu suka bari da marayu, ana barin zane tun ran gini. Ma’ana mace ba sai ta jira matsala ta faru kafin ta nemo magani ba. Matan aure su rike sana’a a cikin gidanjensu idan ba ma’aikata ba ne, yin hakan zai ba ki damar magance lalurorinki masu yawan gaske, ba komai ne za ki rika tambayar miji ba, idan Allah Ya hore miki ma sai ki rika tallafa wa mijin idan ya shiga wani hali. Sannan ki jajirce, ki dauki matakin rarrabe riba da uwar kudi don ki san ci gaban da kike samu. Zai fi kyau ki rika sanya kudinki a asusu irin na gargajiyar nan, saboda kada ki rika zara kina cinyewa. Idan sun yi yawa ki kai banki. A haka sai ki ga abubuwanki na tafiya yadda ya kamata.

Burina a gaba

To a yanzu dai babu abin da nake buri fiye da habaka wannan kamfanin na burodi ya bunkasa ta yadda zai ishi al’ummar Abuja baki daya (dariya). Sannan ina da burin harkokin siyasa, ba wai in tsaya takara ba, a’a, amma ina da wannan burin.

Iyali

Ina da ’ya’yana uku. Maza biyu mace daya kuma dukansu suna makarantar sakandare, amma shi babban zai gama a bana.