✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Illar amfani da na’urori masu haske ga idon yara

Da gaske ne kayan zamani na sadarwa irin su waya da Ipad za su iya bata idon yara? Daga Maimuna Aliyu, Jos Amsa: Eh, ai…

Da gaske ne kayan zamani na sadarwa irin su waya da Ipad za su iya bata idon yara?

Daga Maimuna Aliyu, Jos

Amsa: Eh, ai ba yara kadai ba ma har da manya kayan lantarki na zamani masu haske irin su ‘game’ da wayar hannu da Ipad da Laptop da talabijin za su iya yin illa idan ana dadewa ana kallo. Da yake idanun yara ba su yi kwari ba kamar na manya, tunda suna cikin halin girma, illar ta fi yawa a idanun su yaran. Hukumomin lafiya sun ba da tabbacin cewa in dai ana dadewa ana amfani da wadannan kayayyakin zamani, dadewar da ta zarta awa biyu a rana, to hasken na’urorin za su iya yin illa ga idanu. Dole ke nan sai ana yi ana bibiyar irin dadewar da yara kan yi suna wasa da wadannan na’urori.

Za a ga ba a yi maganar littattafai suna bata ido kamar yadda wadannan na’urori ke batawa ba saboda shi littafi ba ya fitar da haske. Wato yawan karfi da dadewar shigar hasken ke nan ita ce illar ga idanun. Akwai tabarau (gilashin ido) a yanzu na zamani masu tare karfi da illar hasken da masana aikin lafiyar ido sukan ba mutane masu yawan amfani da wadannan na’urori shawara su rika saya suna sakawa yayin da suke amfani da su. Wadannan tabarau daban suke da tabarau masu kare hasken rana, wadanda za a ga su idan an shiga rana suna yin duhu.

Ina da juna biyu sai na yi mura da tari na je asibiti aka ba ni magani ba tare da an yi mini wani gwaji ba, duk da cewa na bukaci a yi mini hoton kirji saboda matsanancin tari da ciwon kirji.

Amsa: Eh, ai ba kasafai a kan so mai juna biyu ta kusanci dakin hoto na D-ray ba ballantana har a haska mata na’urar a jikinta saboda tsoron maganadisun na’urar kan iya illa ga abin da ke ciki, ta hanyar nakasa wani sashe na jiki, musamman ma idan bai girma ba sosai. Shi wannan maganadisun da na’urar kan fitar ko a manya ma zai iya yin illa a wasu lokuta ballantana a dan tayi. Ina ga saboda juna biyun ne ba a yi miki wani hoto ba. In dai an duba an leka an auna an sa abin sauraro an gano matsalar, ta wadatar.

 

Da gaske ne rashin isasshen jini a jikin mace zai iya sa jinkirin al’ada?

Daga Hafsat M. Kaduna

Amsa: Eh, da gaske ne karancin jini a jikin mace wanda rashin isasshen abinci mai kara jini ko yawan zubar jini a wani wuri a jiki zai iya sa mace ta nemi al’adarta ta rasa har sai jikinta ya samu isasshen jini kafin al’ada ta dawo. Wannan wani tsari ne da jiki yake da shi domin tattalin jinin jiki. Wato idan babu jini a jiki to mene ne fa’idar zubar da dan wanda ake da shi?