✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Illar dogaro da gwamnati

Hakika zukatan wasu dimbin Jama’a na mutuwa sakamakon yadda suke dogaro ga gwamnati na ganin sai ta samar musu da aikin yi. An kuma fi…

Hakika zukatan wasu dimbin Jama’a na mutuwa sakamakon yadda suke dogaro ga gwamnati na ganin sai ta samar musu da aikin yi. An kuma fi samun hakan ne musamman ga wadanda suka kammala karatu walau na Sakandire da difuloma da shaidar Koyarwa ta kasa (NCE) Babbar di8fulama (Hnd) da Digiri da sauran su. Domin mafi yawan su sun yi karatun ne da zimmar su yi aikin gwamnati. Domin suna ganin a nan ne kawai za su samu kudi a saukake.Shi ya sa suke raina sana’o’i. To sai dai a nawa hangen ina ganin akada, a raya komin dadewa wata rana jifa kasa za ta dawo.
 Dole masu raina sana’o’i  su dawo su rungume su ka in da na’in. Duba da da yadda a duk shekara ake samun dimbin wadanda suka kammala karatu  sun zura wa gwamnati ido da ta samar musu aikin yi, wanda hatta na gaban su ba su samu aikin ba. Haka wata shekarar wasu na bayan su, su ma za su iske su suna jiran gawon shanun su ma sun ce aikin na gwamnati suke jira. Haka ake ta kara yawa aikin kuma yana kara karanci.
Masu wannan dabi’a ta fifita aikin gwamnati a kan kowace sana’a, sukan jawo ma gwamnati bakin jini tare da suka daga masu jiran sai ta ba su aikin yin. Domin suna jiran a ba su aikin yi tsawon shekara da shekaru kullum suna ganin kamar za su kama-za su kama, sai shiru suke ji. Masu karatu irin wadannan masu jiran gawon shanu suna ganin ai su suna da karatu ya ya za a ce su zo suna yin sana’a? Sai dai wasu daga cikin su Allah yana yi musu gyadar dogo,ta hanyar sake wa kansu tunani da kuma cire girman kai. Sai su rungumi sana’a komin kankantar ta. Kuma cikin ikon Allah suna nan, suna jujjuya dan taro sisin da suke da shi a sana’ar sai likkafa ta yi ta yin gaba.
Domin dama idon ka tashi haikan da nema sai Allah Ubangiji ya taimaka maka.Haka lamarin ke tafiya, wanda a karshe su wadancan da ke jiran aikin gwamnatin wata rana sai su zo wurin ’yan uwan su masu sana’a neman wani taimako ko rance. Saboda haka nake kara bai wa ’yan uwana musamman matasa da ke ganin suna da kwalin karatu shawara, ya kamata su daina raina sa’ana komai kankantar ta.
Da jarabawa dai jirgin sama ya tashi. Kuma masu iya magana na cewa, ‘Mai dukiya kiyayi mai nema.  Wannan magana tasu haka take. Sai dai jiran gawon shanun da wasu ke yi, wasu ke nan masu kammala karatun su ke da wuya za su rungumi sana’ar domin tsira da mutuncin su. Kuma mafi yawan su sukan yi haka ne domin lura da yadda ’yan uwansu da dama ke neman aikin, amma yana gagarar su samu. Bugu da kari kasashe da dama na fama da ta tabarbarewar tattalin arziki, wanda hakan ya sa wasu jihohi ma ba sa iya biyan ma’aikata albashi akan lokaci.
 A karshe ina kara kira da babbar murya ga ’yan uwana matasa da mu cire girman kai, mu kama sana’a ko ya take indai ba ta saba wa doka ba. Domin mu tsira da mutuncin mu, kuma mu kara samun kima da martaba a idon duniya. Da fatan Allah Ubangiji ya kara taimaka mana a duk inda muke, albarkacin fiyayyen halitta.
Daga. Haruna Muhammad Katsina. Shugaban Kungiyar Muryar Jama’a.Reshen Jihar Katsina.  07039205659 [email protected].