✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Illolin yaudara a tsakanin samari da ’yan mata (2)

Bayan fitowar rubutun da na yi a ranar Juma’a 18 ga Janairu 2019, a wannan shafi mai albarka na Iyayen Giji mai taken: “Illolin yaudara…

Bayan fitowar rubutun da na yi a ranar Juma’a 18 ga Janairu 2019, a wannan shafi mai albarka na Iyayen Giji mai taken: “Illolin yaudara a tsakanin samari da  ’yan mata”  na samu kiraye- kiraye da sakonni da dama a kan ya kamata su ma  ’yan matan a zayyano irin tasu yaudarar da sukan yi wa maza. Ga kadan daga ciki kamar haka:

  1. Ko ka san duk macen da take jan kafa wajen gabatar da kai a gaban iyaye ko magabatanta; to ba aurenka za ta yi ba?
  2. Ko ka san duk yarinyar da ta fiye son ka fita da ita zuwa shakatawa musamman wajen shan Ice cream to ba son Allah da Annabi take yi maka ba?
  3. Ko ka san duk yarinyar da ta cika tambayarka kudin yin anko ko kudin kashewa to ba ta damu da kai ba, wani can take so?
  4. Ko ka san duk yarinyar da kullum labarin dukiyar gidansu take yi, to juya ka za ta yi idan an yi aure?
  5. Ko ka san duk yarinyar da take tara samari ta ki fitar da daya to mayaudariya ce, kudinka kawai take so?
  6. Ko ka san duk yarinyar da ba ta son ku yi hira/zance a gidansu, to sheke aya kawai take so ba aure ba?
  7. Ko ka san duk yarinyar da take son a yi hirar surar jikinta, to son sha’awa take yi maka ba son aure ba?
  8. Ko ka san duk macen da ta fiye yin zancen wani a lokacin da ka je zance, to so take ku rabu ba ta sonka?
  9. Ko ka san duk macen da ta fiye yin magana a kan manyan wayoyi, to gaf take ta watsar da kai idan ba ka saya mata ba?
  10. Ko ka san duk macen da ta fiye son taba ka idan kuna hira tabbas ba macen aure ba ce?
  11. Ko ka san duk macen da kullum hirarta a kan tara abin duniya ne, to da wuya ta iya zaman aure?

Wadannan da wasunsu na daga cikin hanyoyin yaudara da mata ke amfani da su wajen yaudarar maza. Sai dai duk da haka akwai salihan matan da suke jiran tsayayyen namiji don su yi aure ba tare da bata lokaci ba.  Amma da yawan wadansu kwadayin abin duniya  da ruwan ido ne ke sa su yi kwantai, a karshe sai su yi nadama da kin bai wa masu sonsu na gaskiya dama.

Lallai tsoron Allah da kyan halinki na taka rawa  wajen samun nagartaccen namiji da zai rike ki tsakani da Allah. Shi kuwa zaman dagawa da sheke aya da burin sai kin auri mai abin duniya, ba abin da yake haifarwa sai nadama. Allah Ya datar da mu.

Ibrahim Hamisu, ya rubuto ne daga Kano za a iya samunsa a 08060651676.

Email. [email protected]