✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Imam Malik: Makarantar kyawawan dabi’u ne (1)

Daga Hudubar Sheikh Abdulbari Assubaitiy Masallacin Annabi (SAW), Madina     Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi…

Daga Hudubar Sheikh Abdulbari Assubaitiy

Masallacin Annabi (SAW), Madina

 

 

Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi mai girma da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka ya ku ’yan uwa Musulmi! Yin magana game da manyan malamai ba abu ne mai sauki ba, kuma ko ka yi kokarin tsakuro wani abu daga rayuwar daya daga cikinsu da wuya ka yin hakan. Domin kana iya barin wasu muhimman abubuwa masu ban sha’awa da suka shafi rayuwarsu.

Rayuwar manyan magabatan malamai babbar abar misali ce da za ta karfafa matasanmu ta yadda za ta hana su koyi da miyagun mutane wadanda ba su da wani abin kirki da za su nuna a wannan rayuwa ko wani abin kirki ga tarihin rayuwar dan Adam.

Maganarmu a kan malamai ba ta nufin karkata ga dayansu ba ce, domin kowane mutum ana iya karbar maganarsa ko a yi watsi da ita, face maganganun Shugabanmu Annabi Muhammad (SAW).

Wanda za mu yi magana a kansa a yau shi ne babban malamin nan Imami a fagen ilimi wanda ya taso a birnin Madina, wanda ambaton sunansa yake faranta rai, kuma iliminsa ya cika bayan kasa. Ya koyar da mutane a cikin Masallacin Annabi (SAW), inda ya yi fice sosai ta yadda in aka ce: “Malamin Madina” ko “Imamu Darul Hijira” ba wani ake nufi ba face shi.

Malik bin Anas (Allah Ya kara masa yarda), an haife shi ne a birnin Madina, ya tashi a can a matsayin mai so da neman ilimi duk da halin da talaucin da yake ciki. Mahaifiyarsa ta yi masa kyakkyawar tarbiyya inda ta umarce shi da cewa” “Ka je wurin Rabi’ata ka koyi kyawawan dabi’unsa kafin ka nemi ilimi.”

Wannan mace ta san nauyin da ke kanta a rayuwa da kuma wajibcin da ke kanta na ilimantarwa da tarbiyyantar da matashin danta. Ta san cewa kyawawan dabi’u su ne kyawawan abokan tafiyar ilimi, kuma ilimi ba ya da amfani idan babu kyawawan dabi’u a tare da shi. Wannan uwa ita ce ta san hanyar gina mutum kuma ta haka sai ta gina kasa.

Gudunmawar da uwa take bayarwa ga tasowar ’ya’yanta ba ta tsaya a kan rainon gangar jiki kadai da kare shi daga cututtuka ba. A’a, tana da babban aikin da ake so ta cimmawa. Aikin ya hada da karfafa imani da gina kakkarfar mutumtaka da bunkasa tunani da ilimi da kuma karfafa wa ’ya’ya su zamo masu martaba. Dukan wadannan ba za a same su ba face tun farko an fifita cusa musu kyawawan ayyuka da dabi’u a zukata a yayin yi musu tabiyya fiye da damuwa da tara abin duniya.

Wannan shi ne hakikanin abin da ya faru a rayuwar Imam Malik (RA), kuma wannan ne ya sanya shi kansa ya zama wata makaranta ta kyawawan dabi’u da daliban ilimi suke koyi da shi, kuma daukacin al’umma take cin gajiyarsa.

Imam Malik (RA) ya taba fada wa wani matashin Bakuraishe cewa: “Ya kai dan ummata! Ka koyi kyawawan dabi’u kafin ka koyi ilimi.”

Yahya bin Yahya At-Tamimi ya ce: “Na zauna tare da Imam Malik na tsawon shekara daya bayan na kammala karatuna a wurinsa domin in koyi kyawawan dabi’u da kyawawan halaye daga gare shi. Kuma halayensa irin na sahabban Annabi (SAW) ne da wadanda suka biyo bayansu.”

’Yan uwa a cikin imani! Hanyoyin koyar da ilimi na zamani a wasu lokuta sukan nuna cewa sun yi nesa da duk wani abu da ya shafi kyakkyawan hali, wanda hakan ya sanya ilimi ya rasa kimarsa da tasirinsa ga mai shi. Idan aka raba ilimi da kyawawan halaye – to duk yawan ilimin da za a samu – za a ga babban tasgaro kan tasirinsa ga halayen mutanen ko tsabtace ayyukansu.  Don haka babu alheri a cikin ilimin da ba za a samu kyawawan halaye ba.

Haifar da gibi a tsakanin ilimi da kyawawan halaye yana haifar da miyagun dabi’u kamar suka da bata malamai da zafafa magana a kansu da mugun hali da wulakanta iyaye da makauniyar biyayya ga kafirai a al’amuran da suka shafi sutura da ta’addanci a kan malaman makaranta da masana ilimi ya alla ta jikinsu ko fadin miyagun maganganu a kansu.

Madina birnin Annabi (SAW) ta bayar da gagarumar gudunmawa a rayuwar Imam Malik (RA), saboda cike birnin yake da manyan malaman Musulunci. Masallacin Annabi (SAW) shi ne makaranta ta farko a tarihin Musulunci, kuma a kowane lokaci akwai ajujuwan da ake koyar da ’ya’yan Musulmi kyakkyawan ilimi da ke ba su damar kasancewa masu ilimin addini kuma masu kyawawan halaye da dabi’u.

Ya ’yan uwa Musulmi! Abu ne sananne cewa abin da mummunan muhalli (mugun abokin zama) yake yi shi ne lalatawa ba ginawa ba. Idan ba haka ba, mene ne amfanin koyar da yaro kyawawan halaye da dabi’un Musulunci safe da maraice amma sai ya je wurin miyagun abokan zama da za su rusa abin da iyayensa suka dasa masa? Ko kuma mene ne amfanin koyar da yaro kyawawan dabi’u na shekara da shekaru amma sai wannan mahaifi nasa ya kai shi muhallin da yake cike da almundahana?

Kafin Imam Malik (Rahimahullahu) ya zauna ya fara bayar da fatawa sai da manyan malamai saba’in suka tabbatar da cancantarsa a kan haka. Ku dubi bambancin da ke tsakanin wanda yake yabon kansa kuma yake cuccusa kansa a san da shi da wanda iliminsa ya jawo masa yabo kuma ya kai shi cikin zababbun mutane. Imam Malik (Rahimahullah) ya ce: “Ba kowane mutum da zai so ya zauna a masallacin ya koyar da Hadisi kuma ya bayar da fatawa ba ne ya cancanci haka. Mai son ya zauna ya bayar da fatawa ya fara da neman shawarar salihai da zababbun mutane; idan suka ga ya cancanci haka sai ya fara; domin ni ban zauna in fara koyar da Hadisi ko in bayar da fatawa ba, sai da malamai saba’in suka tabbatar da cancantar yin haka.”

Imam Malik (Rahimahullah)  ya ce: “Ni mutum ne kawai, nakan yi kuskure kuma nakan bayar da fatawoyi daidai. Idan na bayar da fatawa ku auna su, idan sun dace da Sunnah ku karbe su.” Da wannan muhimmmin bayani, Imam Malik (Rahimahullah) ya nuna madaidaiciyar hanya ta bi a tsakanin masu yin makauniyar biyayya ga shugabanni da wadanda suke watsi da ingantaccen nassi da maganganun malamai, suna cewa: “Su ma mutane ne, mu ma mutane ne.” Mene ne bambancin wadancan mutane da wadannan mutane?  Mene ne bambancin mutanen da suka rasu wadanda Allah Ya girmama sunansu na karnoni da mutanen da ba su da wata daraja da suke masu rai ne da za a iya kirga su da matattu? Ambaton sunayen wadannan malamai na farkar da zukata, mutum ya rika jin kamar yana tare da su a zuciyarsa. Wadannan manyan malamai ba ilimi suke da shi kadai ba, a’a su shugabanni ne a fagen kyawawan halaye da hakuri da muru’a da kamun kai da kuma tsoron Allah!

Sai dai kuma akwai wadansu daga cikin mabiya wadannan malamai wadanda suka zabi su takaita kansu ga taklidi ba su su son su kara gusawa gaba duk da cewa za su iya bambancewa a tsakanin karya da gaskiya.

Kuskure ne ka rika tozarta ayyukan sauran mutane, ko ka rika jin aikin kirkin wani ya fi na saura. Wannan saboda ilimi da gogewa baiwa ne daga Allah ba daga wani mutum ba. Wannan shi ne babbar fahimtar da Imam Malik (Rahimahullah) yake son nuna wa jama’a cewa yi wa Musulunci hidima aiki ne da ke kan kowane Musulmi a duk bangarorin rayuwa ba tare da wani ya yi tawaye ko adawa ga sauran Musulmi ba. Imam Malik (Rahimahullah) ta rubuta wa wadansu masu ibada a zamaninsa cewa: “Allah Ya karkasa ayyukanmu kamar yadda Ya karkasa baiwarmu (fasaharmu). Wadansu Ya ba su karfin jiki za su iya yi nafilfili masu yawa, amma ba a ba su baiwar yin azumin nafila ba; wadansu kuma an albarkace su da iya yin azumi, wadansu da jihadi, wadansu da neman ilimi. Yada ilimi yana daya daga cikin kyawawan ayyuka kuma ina jin Allah  Ya albarkaci wani da wani abu kuma ba na jin abin da nake yi ya fi abin da kake yi, sai dai fatata dukanmu biyu muna aikata kyawawan ayyuka.”