Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

In za ka gina ramin mugunta… (1)

Wata mata ce ana kiranta delu tana da da mai suna Auwal sai kuma dan mijinta wanda ake kira Sani. To shi Sani mahifiyarsa ta rasu don haka delu ce ke rikonsa.  Sani yaro ne mai biyayya ba ya tsalalke duk abin da delu ta gindaya masa, sai dai duk da wannan biyayyar da yake yi mata ba ta gani saboda ba ta kaunarsa.

Da zarar Sani ya yi kuskuren yi mata laifi yini sai ta yini tana yi masa fada, shi kuwa mijinta sai dai ya  yi ta ba ta hakuri saboda da ma tsoronta yake ji.

ADVERTISEMENT

Allah ya sanya soyayyar ’yan uwantaka a tsakanin Auwalu da Sani duk da cewa delu ba ta son wanann shakuwar tasu.

A lokuta da dama takan yi wa Auwalu fada ya daina kula Sani, shi kuma yakan nuna mata cewa shi ma Sani yana kaunarsa don haka ba zai daina kula shi ba.

ADVERTISEMENT

Wata rana delu tana zaune tana tunanin yadda za ta raba danta Auwalu da Sani, ganin ta yi iya bakin kokarinta ta hanyar bin bokaye da ’yan tsibbu amma ta kasa raba tsakaninsu sai ta yanke shawarar kashe shi ta hanyar sanya masa guba a cikin abinci.

Mu kwana nan