✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina barayin suke? (3)

Ke nan harkar sata a Najeriya ta riga ta zama ruwan dare, domin kuwa ba ta bar kowane shugaba da tsarin shugabancin da yake yi…

Ke nan harkar sata a Najeriya ta riga ta zama ruwan dare, domin kuwa ba ta bar kowane shugaba da tsarin shugabancin da yake yi ba. Ina shugabannin kwadago? Ina shugabannin ’yan yuniyon da masu tura baro da masu faskare da ’yan-ga-ruwa da shugabannin mata masu adashi da kungiyar malamai tun daga firamare zuwa sakandare da jami’o’i? Ina maigida da gidansa, ina matarsa da ’ya’ya, ina mai sayar da man gyada da tumatir a kasuwar kauye? Su wadannan ba barayi ba ne?
Ba sai mun tsaya wani dogon tunani ba, yanka musu ragon sunan da ya dace da su, barayi ne, sak, tun daga sama har kasa! Idan kana son ka tabbatar da haka, to je ka inda ake zaben shugabannin kungiyoyin kwadago ka ga yadda ake kai kawo da dukiya don a zabi wane ko kuma wance. Kwanakin baya Shugaba Jonathan ya kori Ministan Harkokin Matasa saboda ya shiga dumu-dumu cikin harkar zaben Tarayyar kungiyoyin Matasa ta kasa, kudi da giyar mulki da sata su ne ruhin irin wannan zabe, ba a kuma tsammanin shugaban da aka zaba bisa ga wannan mukami bayan ya zuba jari, ya ce ba zai mayar da uwar kudinsa ba, har ya ci riba. Ba kuma hanyar da zai bi ya yi haka, sai ta sata ko fashin dukiyar al’umma ko ta gwamnati. Haka abin yake a yawancin kungiyoyin kwadago da ake da su. Idan ka ji ana fada da zare ido da hayaniya wajen zaben shugabanni, ba wai don aikin da ake wa mutane ya yi yawa ba ne, sai dai don yawan satar da ake yi ta yi yawa ne, dole kuma a irin wannan yanayi a ba hammata iska, a gwabza, har ma a kashe domin samun sararin yin satar da kyau.
Haka abin yake a tsakanin kungiyoyin ’yan yuniyon ko na tasi ko na bas ko na ’yan acaba ko na masu hayar keke. Ko na magina ko na kasuwanci ko makamnantan haka. Me ya sa shugabanninsu ke kasancewa masu kudi fiye da sauran ’yan kungiyar? Me ya sa da su can tun farko talakawa ne kamar saura, amma da sun haye kujerar shugabanci sai su kasance hamshakai? Me ya sa da sun fara da yaran mota in a kungiyar yuniyon ne, daga baya za su kasance dirobobi da sun hau kujerar shugabanci, shi ke nan sun yi ban kwana da talauci, su da ganin sitiyari sai in sun hau tasu motar mai cike rabar jin dadi da annashuwa, suna ofis, sai kwasar garabasar shugabanci? Ba wani abu suke yi ba sai wandaka da dukiyar talakawansu, irin wadannan me ya bambanta su da minista ko kwamishina ko kuma dan kwangila? Duk dai mota daya suke yawo a cikinta, mota ce da bakin dare ke tukawa lokacin da kafa ta dauke!
Mu duba da kyau, me ya sa uwar adashin mata, kai har da uban adashi ke kasancewa sarki ko sarauniya a cikin wannan harka? Me ya sa idan ka ga gungun almajirai na yawon bara sai ka ga Naira 100 ta wargaza tarayyarsu? Da an samu wani ya bayar da kudin bara, idan ya ce ku je raba, to, in ba a yi hankali ba, shugaban almajiran sai an yi daga da shi wajen rabon, ko dai ya kwashe rabi ya raba wa ‘talakawan nasa’ abin da ya rage, ko kuma a shiga cece-ku-ce har sai manya sun shiga maganar, ko a kare gaban ’yan sanda don a raba gardama? Me ya sa? Saboda ba gaskiya almajiran suka taka ba. Shi kansa shugaban almajiran barawo ne; ’yan uwansa su ma iyalinsa ne, kar ce ta san kar, ita ce kuma ke kallon kar a cikin al’umma. Domin kuwa su kansu almajiran na kallon mai ba su barar a matsayin barawo, wato dole ta sa yake debowa daga abin da ya sato, ya zo wurin su neman lada daga Allah.
Irin haka ke faruwa a tsakanin ’yan sanda da sojoji da duk wasu masu kaki ko kayan sarki ko malaman firamare ko na sakandare ko na jami’o’i. Daga oga zuwa karabiti ba wanda tabon satar nan ya bari. Shi dan sandan da ke bakin hanya ko kurtu da sajan soja da ke tsare rayukan mutane bakin titi me ya raba su da oga da ke cikin ofis ko a karamar hukuma ko a babban ofis a babban birnin jiha ko kuma a can Abuja? Abin da ya bambanta su kila shi ne yawan nauyin aljihunsu, wani shagwal aljihun yake, wani kuma tinjim! Shi ya sa in na ga malamin firamare ko na sakandare ko na jami’a na zagin dan sanda ko soja ko kwastam ko imigireshin, dariya abin yake ba ni, wanne ne ba wanne ne ba! Tambayi iyaye da dalibai ka sha labarin irin satar da ake tafkawa a cikin makarantu. Kudin gyaran jarrabawa! Kudin aza yara bisa matsayin da ba nasu ba ne! Kudin satar jarrabawa! Kudin sayen littattafan karya! Kudin, kudin, kudin…..ga su nan ba sa lissafuwa!
To amma sai ka tambayi kanka, me ya sa malami zai lalace haka, har a gane cewa shi ma barawo ne? Ba wata hujja face, shi ma ya fahimci ai duk kanwar ja ce. Yaron da ake neman a taimaka wa dan karamin barawo ne! Ita uwar da ke biye da malamai a taimaka wa yaron, makimanciyar barauniya ce! Shi uban da ke bayar da kudin a gyara, ko a taimaka wa ’ya’yan nasa, barawo ne! Ke nan duhu ne ke gugar duhu! Ba kuma inda haske zai fito a cikin wannan kwamacala!
Ke nan matar nan da ke kauye tana sayar da gurbataccen man gyada, ta san abin da take yi, barayi ne ke zuwa daga garuruwa don su saya, su je su surka da kwantarola su sayar wa wadansu barayin da ke kimshe a cikin birane. Idan ta yi laifi, mene ne laifinta? Shi ya sa yawancin miyar da muke sha a cikin gidaje take kasancewa ba ta tayar da komadar iyali. Gurbataccen man gyada ne daga gyadar da aka noma daga kudin sata! Shi ya sa yanzu ’ya’ya ba sa jin tausan iyaye, domin kuwa sun ci sun sha daga dukiyar haram. Rigar haram! Wandon haram! Abin hawan haram! Gidajen haram! Cefanen haram! Tuwo da miyar haram! Iyayen haram? Rayuwar Haram?
Ina mafita? Wallahi ban san yadda za a yi ba, ban san mafita ba daga dankali mai sankara, domin kuwa haka rayuwar tamu ta kasance a yau. Duk inda ka sa wuka kana debe ciwon sankarar da ke cikin dankali, za ka kare ne da cire dukkan dankalin, domin ya lalace, abin da zai rage daga dankalin mai kyau bai da yawa! Amma ina da yakinin wani abu guda da zai iya zama mafita, ita ce mu amince cewa dukkanmu barayi ne! Lalatattu ne! Munafukai ne! Macuta ne! Mahandama ne! Mu gwada mu gani ko za a samu mafita ta wannan hanya! NI DAI NA YARDA, NI bARAWO NE! KAI FA? KE FA? KU FA?
Za mu ci gaba