✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina da kyakkyawar alaka da ’yan fim  – Afakallah

Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’ila Na’abba Afakkalah ya ce akwai fahimtar juna a tsakanin hukumarsa da ’yan fim din masana’antar Kannywood.…

Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’ila Na’abba Afakkalah ya ce akwai fahimtar juna a tsakanin hukumarsa da ’yan fim din masana’antar Kannywood.

Isma’ila Afakallah ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Aminiya, inda ya ce, “Akwai kyakkyawar fahimta tsakanin jaruman masana’antar da hukumarsa, sai dai kawai wadansu tsiraru ne da ba sa ganin alherin da muke kokarin kawowa duk  da cewa saboda su muke yi. Don haka ina tabbatar maka cewa saboda wannan kyakkyawar alaka da muke da ita ce ma har muka samun nasarar fara tsabtace masana’antar ta hanyar yi wa jaruman rajista da kuma lura da dukkan ayyukansu. Mun kuma samu nasarar gudanar da zabubbuka ga kungiyoyin masana’antar domin samun hadin kai.

Ya ce “Lokacin da muka zo, wato lokacin Gwamna Abdullahi Ganduje na farko, mun samu masana’antar babu tsari, kowa na da dama ya zo ya yi abin da ya gadama ya tafi, wanda hakan ke jawo rikice-rikice da yawa. Wannan ya sa muka ce muna son sanin jaruman baki daya, na bukaci a kawo min sunansu duka, amma babu. Wanda hakan ya sa muka kafa kwamiti domin rajista da bayar da lasisi.

Haka kafin nan akwai wasu munanan dabi’u da wadansu da suke cewa su ma ’yan Kannywood ne suke aikatawa da ke bata sunan masana’antar. Duk abubuwan nan ne suka sa muka ce duk wanda yake sha’awar yin harka a Kano, dole ya samu lasisi daga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano.”

Game da batun cewa akwai son kai a wajen hukuncin hukumar, sai ya ce wannan kawai zargi ne da babu tabbas, “Duk wanda yake wannan zargi ya kawo misali. Ba mu ba ne muke hukunci, idan mun ga laifi, kotu muke kai mutum. A iya sanina babu wanda ya yi laifi muka bar shi,” inji shi.

Kan batun bidiyo da ake sanyawa a manhajar YouTube, Afakallah ya ce hukumar na kula ne da duk wani abu da za a saka zuwa ga mutane matukar fim ne, dole a tace, ko a YouTube ko a CD.

Kan batun rufe shagon hoto na Sani Danja (Celebrity Photos), Afakallah ya ce “An rufe har da Balancy da sauran 30. Me ya sa za mu bar nasa? Amma da ya zo ya yi abin da ya dace, ba an bude masa ba? Ka je ka duba yanzu,” inji shi.

Kan batun Adam A. Zango, Afakallah ya ce Zango ya ce ya fice daga Kannywood, kuma lokacin da zai zo kallon fim din Mati A Zazzau, da ya sayi tikitin kallo, ya zo ya yi kallonsa da babu ruwansu da shi, “Amma da ya ce yana kira ga masoyansa su zo su kalli fim din tare da shi, kuma zai raba musu kyauta, wannan ya zama taro ke nan. Kuma idan zai yi taro, dole sai ya rubuto mana takarda, inda za mu ba shi ka’idojinmu, amma bai yi ba. “