✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina da yakinin zan zama Gwamnan Bauchi a 2019 – Sardauna

Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PPN, Alhaji Bello Sa’idu Sardauna ya ce yana da yakinin shi ne zai lashe zaben Gwamnan Jihar…

Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar PPN, Alhaji Bello Sa’idu Sardauna ya ce yana da yakinin shi ne zai lashe zaben Gwamnan Jihar a 2019 idan Allah Ya so, kasancewar shi ya fi kowa cancanta a cikin ’yan takarar.

Alhaji Bello Sardauna ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya ke zantawa da wakilinmu a Bauchi ranar Lahadin da ta gabata, ya ce jama’a suna kara wayewa kan harkokin siyasa wajen tantance ’yan takarar da suka cancanta ba tare da la’akari da jam’iyya ba.

Kan yaya zai fuskanci APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP a 2019, sai ya ce tuni al’ummar Jihar Bauchi suka dawo daga rakiyarsu, “Domin idan ka kula Gwamna MA Abubakar bai kulla komai na ci gaban jama’a a jihar ba, illa kawai hamayya da ’ya’yan APC, ya bata da kowa sannan ba ya da kowa. Ita kuma PDP dama tuni an gaji da ita.  Da wannan ne al’ummar Bauchi musamman matasa da kansu suka bukaci in fito takara a karkashin kowace jam’iyya, sannan suka yi alkawari za su fito su zabi cancanta maimakon jam’iyya,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa “A lokacin zaben 2019 masu kada kuri’a za su fito kwansu da kwarkwatarsu kuma za su jefa wa cancanta, kuma mu matasa mu ne za mu iya magance matsalolin a’ummarmu yadda ya kamata, kuma ina da manyan manufofi da za su ciyar da Bauchi da al’ummarta gaba wadanda shugabannin baya ba su mai da hankali a kansu ba.”

Dan takarar ya yi fata Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar da zaben na 2019 bisa gaskiya da adalci ba tare da tauye wa kowane dan takara ko jam’iyya hakkinsu ba.

Ya ce “Bisa ga abin da ya faru a fadin kasar nan tun lokacin Farfesa Jega na shugabancin INEC, da kuma shugabancin Farfesa Mahmood Yakubu, ina da yakinin cewa za a yi zabe na gaskiya, kuma jami’an tsaro, da’ yan jarida da sauran bangarorin da suke da ruwa-da-tsaki kan sha’anin zabe za su tabbatar da an yi sahihin zabe mai cike da adalci.”

Sardauna ya ce ba yana neman zama Gwamnan Jihar Bauchi don kansa ba ne, sai dai saboda burin da yake da shi na gyara kura-kuran da aka tafka a baya da kuma sauya tsarin da yake hana jihar ci gaba, tare da dora jihar da jama’arta kan turbar da ta dace.

Dan takarar ya bayyana cewa Jihar Bauchi a halin yanzu ta gaza samun tsarin da zai kawo sauyi a sashin ilimi da lafiya da noma da sauran muhimman abubuwan da ya ce dole ne su shiga domin kawo gyara da cire jihar daga mawuyacin halin da ita da al’umma suka kasance cikin talaucin da za a iya kauce masa.

Dangane da wadanda ba su amshi katin zabensu ba, Alhaji Sardauna  ya ce muddin mutum bai samu ya amshi katin  zabensa ba, babu yadda zai yi wajen sauya mulkin rashin adalci, kuma babu yadda zai yi wajen kawo nagartattun shugabanin da yake da yakini a kansu. Don haka ya nemi jama’a su tashi tsaye wajen amsar katinsu na zabe wanda shi ne ’yancinsu.

A karshe ya ce watanni kalilan suka rage ya zama       Gwamnan Jihar Bauchi,  bisa haka ya nemi al’ummar jihar su zabi jam’iyyarsau ta PPN a jihar da kuma dogarin marigayi Shugaban Kasa Janar Sani Abacha, wato Manjo Hamza Al-Mustapha da yake yi wa jam’iyyar takarar Shugaban Kasa a zaben da ke tafe.