✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina goyon bayan rufe kan iyakoki – Sarki Sanusi

Mai martaba Sarkin Kano,Malam  Muhammad Sanusi II ya bayyana goyon bayansa kan rufe iyakokin asar nan, inda ya ce hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin…

Mai martaba Sarkin Kano,Malam  Muhammad Sanusi II ya bayyana goyon bayansa kan rufe iyakokin asar nan, inda ya ce hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sarki Sanusi ya kuma yaba wa Shugaban Kasa Buhari kan rufe iyakokin domin hana shigo da abubuwan da ake iya sarrafawa a cikin kasa.

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manama labarai a fadarsa da ke Kano a shekaranjiya Laraba.

Ya ce yanayin yadda iyakokin Najeriya suke a bude ne ya jawo kasar nan ke asarar kudade masu yawa da ya kamata su samu sanadiyar harajin shigo da kayayyaki, kuma yana taimakawa wajen fasakwaurin man fetur.

“Idan ba ku manta ba, lokacin da Shugaban Kasa ya zo Kano, na nanata masa  cewa a rufe iyakar kasar nan da Benin. Na dade ina cewa idan har ana so a tabbatar da doka da hana fasakwauri, dole  a rufe iyakokin kasar nan. Ana fitar da man fetur zuwa kasashen da muke makwabta da su saboda muna da tallafin man fetur, sannan ana shigo da kayayyaki ta Kwatano domin gudun biyan haraji a iyakar Legas. Ke nan ana asarar kudin fito da yawa,” inji shi,

Sannan Sarkin ya yaba wa Shugaba Buhari kan  kafa Kwamitin Kwararru kan tattalin arziki, inda ya bayyana wadanda aka zaba a matsayin kwararru kuma masana tattalin arziki.