✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina goyon bayan soke nade-naden da Dankwambo ya yi – Habu Mu’azu

Alhaji Abubakar Habu Mu’azu Hassan, Yeriman Kashere, jigon dan siyasa ne a Jihar Gombe wanda ya taka rawar gani sosai wajen samun nasarar cin zaben…

Alhaji Abubakar Habu Mu’azu Hassan, Yeriman Kashere, jigon dan siyasa ne a Jihar Gombe wanda ya taka rawar gani sosai wajen samun nasarar cin zaben Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya zama Gwamna kuma shi ma ya kasance daya daga cikin ‘yan takara takwas na Jam’iyyar APC din da suka nemi kujerar ta Gwamna a jihar. A hirarsa da Aminiya ya nuna goyon bayansa matuka ga sabon zababben Gwamnan jihar, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, na soke duk wani nade-nade da kwangiloli da daukar ma’aikatan da tsohuwar gwamnatin ta yi a washegarin barin ta mulki.

Alhaji Habu Mu’azu ya ce yanzu ne al’ummar Gombe za su ga canji da gyara a mulkin Inuwa Yahaya wanda tsohuwar gwamnati ba ta yi su ba.

“Idan aka samu sabuwar gwamnati dama dole sai an dan yi jira don ba a san me za a tarar ba tun da jihar ba kudi take da su ba” inji Mu’azu.

Ya kuma ce abin da ya sa ya goyi bayan rushe duk nade-naden shi ne ba da kyakkyawar manufa aka yi su ba, domin Dankwambo yana da sauran kwana daya a mulki ya yi, inda zai sauka a ranar 29 ga watan Mayu a ranar Talata 28 ga watan, ya dinga yin nade-nade da daukar ma’aikata sama da dubu biyu.

Habu Mu’azu, yace an bar mutanen jihar Gombe da yunwa da fatara yan kwangila sun kashe kudaden su ba a biya su ba ga yan fansho duk ba wanda aka biya shi,don haka, dole Inuwa ya zauna ya fara duba wadannan kafin aiwatar da komai.

Dan siyasan ya kara da cewa a washegarin da Dankwambo zai bar mulki ne ya kirkiro Sarakuna fiye da guda hamsin idan da gaske ne, me yasa a shekara takwas da ya yi bai yi su ba, sai a kwana daya da zai bar gwamnati hakan ne tasa nace ba da kyakkyawar manufa aka yi su ba.

Yeriman Kashere, ya yi amfani da wannan damar ya bai wa Gwamna Inuwa Yahaya shawarin cewa ya yi adalci wajen rabon mukamai a mulkin sa,  ya tsaya ya duba wadanda suka sha masa wahala daga matakin farko har zuwa lokacin da yaci zabe ya zama Gwamna, kar ya sa son rai idan yabi son rai zai kuma ga bacin rai haka abun yake a siyasan ce.

Ya kuma sake yin kira ga al’ummar jihar Gombe da su yi hakuri suci gaba da taya gwamnan da addu’a domin sai da addu’a kuma dole sai ya yarda yana karbar shawara dan kar a ga abunda zai cutar aki magana saboda tunanin ko an gaya masa ba zai karba ba.

Daga nan sai ya ce shi ma gwamnan sai ya yi adalci kuma ya toshe kunnensa daga jin jita-jita don kar ya yarda da masu neman hada shi da mutane. Idan ya bari ‘yan gulma suka yi tasiri, to idan abubuwa suka lalace su ma guduwa za su yi su bar shi, sannan kuma kar ya yi tunanin cewa a baya kafin ya zama gwamna wani ya ci mutuncinsa sai ya rama yanzu shi gwamna ne ya rungumi kowa a tafi tare.