Da Dumi Dumi

Ina noma kadada 10 na Bi-Rana – Dokta Erisa Sarki

Dokta Erisa Sarki

Shugabar Kungiyar Manoman Bi-Rana (Sun Flower), ta Jihar Gombe, Dokta Erisa Sarki Danladi ta ce akwai riba sosai a  noman  Bi-Rana, kuma bai ya da wahalar nomawa kamar masara da sauran amfanin gona, inda ta ce tana noma kadada 10 na Bi-Ranar.

Dokta Erisa Danladi, ta shaida wa Aminiya cewa  abin da ya ba ta sha’awar fara noma  Bi-Rana shi ne ta tashi ne ta ga ana yafa shi a tsakanin dawa ko masara a gona kuma yana yi ana cirarsa ana ci.

Ta ce kafin ta fara noman Bi-Rana, masara take nomawa wadda a shekara takan noma buhun masara 70 da waken soya; amma duk da haka ba ta bar nomansu ba hadawa take yi da Sun Flower din.

A cewarta jihohin Kaduna da Gombe ne Bi-Ranasu ya fi kowane kyau domin shi ne wanda idan aka noma ake fitar da shi kasashen waje saboda kyansa, wanda hakan ne ya sa suka kafa kungiyar manomansa.

Dokta Erisa, ta ce Bi-Rana ba ya son ruwa sosai shi ya sa aka fi noma shi da rani saboda wajen ba shi ruwa za a rika kiyayewa, kuma kilo-kilo ake sayarwa da irin ba buhu-buhu ba.

ADVERTISEMENT

Shugabar ta kara da cewa kowace kadada guda daidai take da kilo daya wajen shukarsa domin tana da kadada 10 da take nomawa ita kadai; sannan a kungiyance suna da kadada 50. Ta ce an fi noma Sun Flower a Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe saboda yanayin kasar wajen.

Shugabar ta ce ana noma shi sau biyu a shekara rani da damina. Kuma saboda cin ribar nomansa ya sa suke yin sa a kungiyance.

Wajen kashe kudi kuwa ta ce a kowace kadada guda za a iya kashe kimanin Naira dubu 120. Domin  samun riba sosai idan aka fitar da shi  kasashen waje, hakan ya sa suka nemo iri mai kyau da inganci.

Dokta Erisa Danladi, ta ce  Sun Flower ana matsar mansa kamar gyada, don yin girki da shi sannan kuma ana cin sa haka.

Ta ce Bi-Rana ya fi son a sa masa takin dabbobi a kan na zamani.

Ta yi kira ga gwamnati ta taimaka musu kamar yadda take taimaka wa manoman masara da taki da irin shuka a kan farashi mai sauki, inda ta ce a baya sun taba  magana da tsohon Ministan Aikin Gona, Mista Audu Ogbeh, inda ya yi alkawarin taimaka musu.

Ta koka kan yadda a baya ta sha rubuta wa gwamnati kan ta taimake su ta an samar da injinan da za su rika sarrafa Bi-Ranar ta hanyar matsar mansa da sarrafa waken soya zuwa abincin yara da sauransu; amma har yanzu shiru.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya