✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ina samun Naira dubu 400 a mako kan noman Strawberry amma…’

Gyang Matthew na daya daga manoman Strawberry wanda ya shafe akalla shekara hudu yana nomanta da ya fara da kadada daya kafin daga baya ya…

Gyang Matthew na daya daga manoman Strawberry wanda ya shafe akalla shekara hudu yana nomanta da ya fara da kadada daya kafin daga baya ya kara zuwa kadada 1.8.

Yana da kadada uku inda a ciki ya mayar da kadada 1.8 wajen noma Srawberry, kadada 1.2 kuma yana noman karas da latas.

Daga kadada 1.8 da yake nomawa na Strawberry, Mista Gyang Matthew yana samar wa da mata da matasa aikin yi a wani kauyen Chaha, inda yanzu haka  akalla yake samun katan 100 a kowane mako inda kowane katan yake da nauyin kilo biyar zuwa shida. Kuma a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu ne ake noman da ake samun yabanya.

Kowane kilo daya na Strawberry ana sayar da shi ne kan Naira 800 a wannan lokaci inda katon 100 ke kaiwa kilo 500 zuwa 600 da akalla yake samun Naira dubu 400 duk mako, a wasu makonnin ma yakan samu fiye da haka kuma sau biyu ake nomansa.

Manomin yana da ma’aikata 14 a gonarsa, inda 10 daga cikin ma’aikatan yake biyansu Naira dubu daya kowace rana, sauran hudu kuma a wata yake biyansu, Naira dubu 18 kowanensu bayan yana ba su abinci sau uku a rana ya kuma ba su wurin kwanciya a gidansa.

A lokacin da yake bayani a gonar bayan ya cire Strawberry din, Mista Gyang, ya bayyana wasu daga cikin matsalolin da suke ci masa tuwo a kwarya duk da yadda yake tunanin fadada noman.

“Yadda na faro noman abin sha’awa ne. Abin da ke kara min kaimin fadada noman shi ne wadannan mata da matasa da nake biyansu kullum, domin duk lokacin da na biya su suna magance matsalolin iyalansu.

Sauyin yanayi yana shafar nomanmu, domin a bara an jima ana ruwan sama da ya kamata a ce mun fara cirar Strwaberry din tun a watan Satumba amma saboda ruwa ba mu iya ba sai da muka kai watan Nuwamba. A tsakanin wata biyun da suka karu mun yi hasarar kudin da muka samu wajen girbi.

Wata matsalar har ila yau ita ce ta sufuri da adana shi, domin a wasu lokutan mukan kai filin jirgin sama don daukarsa zuwa Legas wanda ba a daukarsa da yawa saboda suna dauka ne bisa ga kilo-kilo ga shi kuma a watan Fabrairun nan zan girbi kilo 1,000 wanda shi ne tan guda kuma mafi yawan kayan da jirgin ke dauka shi ne kilo 200, an bar kilo 800 a kasa ke nan wanda aka bari a kasa din idan ka yi lissafin taki da maganin feshi da sauransu da kudin aiki ba karamar hasara ba ce,” inji shi.

Ya ce akalla yana kashe Naira miliyan biyu a sharar gona kadai kafin ya kwantar da bututan ruwa da man gas na janareto da yake ban-ruwa da shi.