✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ina sayar wa fadan shugaban kasa da namun daji’

Abubakar Mustapha (Dogo) Wani dan asalin Unguwar Gwange da ke cikin birnin Maiduguri, amma a halin yanzu yake zaune a birnin  Abuja mai suna Abubakar…

Abubakar Mustapha (Dogo) Wani dan asalin Unguwar Gwange da ke cikin birnin Maiduguri, amma a halin yanzu yake zaune a birnin  Abuja mai suna Abubakar Mustapha (Dogo)  ya rungumi harkar sayar da dabbobin alfarma domin neman  abin da zai rufa wa kansa asiri, kuma ya ce kwalliya tana biyan kudin sabulu.
Abubakar Mustapha ya  shaida wa Aminiya cewa, da farko da ya je Abuja ya rungumi harkar dillacin gidaje ne, amma da ya ga babu ci sai ya buge da sayar da namun daji, inda ya shiga harkar sayar da tsuntsaye gadan-gadan.
 Ya ce ya rungimi harkar ce a lokacin da ya gane cewa manyan mutane wadanda suka ci kuma suka koshi suna neman dabbobi na alfarma ko tsuntsaye don su kara kawata gidajensu da su, kamar  Zaki da Damisa da Kura da Mesa da Jimina da biri da dawisu da Aku, da dai sauransu.
 Abubakar Dogo ya ce suna sayo dabbobin ne daga kasashen Nijar ko kuma Kamaru. Inda ya ce ana kama mutum idan aka ganshi da wadannan dabbobin a kasashen waje, amma a Najeriya komai cikin sauki yake in dai kana da kudi.
 Ya ce mafarauta ne ke kamawa da tarko, su kira su, su kuma su je su saya sai su yi kasadar tsallakowa da su nan kasar.
 Ya kara da cewa, yana sayar wa da fadan Aso-Rock da Gada da dawisu da Kunkuru, bayan da likotocin dabbobin fadan suka tabbatar da cewa suna da cikakken lafiya. Sai a sanya su a filin cikin fadar don nishadi. Ya ce ana sayen su ne idan wadanda ake da su suka mutu, ko kuma ana bukatar kari.
Abubakar ya ci gaba da cewa, yana wasa da ‘ya’yan Zaki kafin su kai shekaru uku, domin idan sun yi farata da fika ba a wasa da su, don suna iya fatattaka mutum.
Ya ce kudinsu yana kamawa daga Naira miliyan uku zuwa sama. Ana ajiye  su ne a kauye, don ciyar da su a birane yana da tsada, musamman ma a gari Kamar Abuja. Ana ba su Akuya ko Kaji su kashe da kansu kafin su ci. Amma idan an ba su nama suna ci, sai dai sun fi son su kashe da kansu su sha jinin.  Amma ita kuwa Kura ko kashi ka ba ta za ta yi kalaci da shi nan take.
 Dangane da Aku kuwa, ya ce zai yi magana idan an kama shi an sayar tun yana karami, kuma idan gidan da yara. kananan Aku suna da farin idanu, amma wanda ya rika yana da ido mai kalar ruwan kwai, kuma ba zai yi magana ba don ya zama buya.
 Ya ce wadanda suka fi sayan dabbobi da tsuntsayen sun hada da masu hali da sojoji da dai sauransu.
Abubakar Dogo Mustapha ya kara da cewa, ya dace gwamnati ta gina babban gidan ajiye namun daji don yaran Abuja su san su muraran.