Search
Subscribe
Ina son ganin mata suna da kamun kai da kima  – Hajara Kabir

Ina son ganin mata suna da kamun kai da kima  – Hajara Kabir

Hajara Kabir ita ce Shugabar Kamfanin  Girke-Girke na The Pastry Kitchen. Matashiya ce  mai shekara 23, ta fito ne daga Malumfashi a Jihar Katsina. Mace ce mai kwazo da hazaka wacce ta yi nasarar fita da Digiri Mai daraja ta Daya (First Class) a ilimin injiniyarncin man fetur da gas daga Jami’ar Nile Unibersity da ke Abuja, kuma tana da himma a fannin kere-kere. A shekarar 2018 an nada ta Jakadiyar  STEM ta Afirka (STEM Ambassador). A hirarta da Aminiya ta bayyana irin jajircewar da ta yi wajen cimma burinta:

Tarihina

Sunana Hajara Kabir Abdulfatah, amma an fi sanina da ‘Ammah.’ Ni ’yar garin Malumfashi ne a Jihar Katsina. An haife ni a watan Satumban 1996, wato shekarta 23. Na yi firamare a makarantar Therbow da ke Zariya sannan na yi sakandare a makarantar Kueen Science Academy da ke Kano. Sannan na tafi Jami’ar Nile da ke Abuja inda na kammala karatu a fannin Injiniyancin man Fetur da Iskar Gas. Yanzu kuma ni ce Shugabar The Pastry Kitchen (TPC).

 Abin da na yi niyyar karantawa

A gaskiya, tun ina sakandare nake da burin zama injiniyar man fetur da gas (Petroleum and Gas Engineering).

Na zabi in zama injiniya ce saboda na yi tunanin karatun zai yi dadi! Kuma ina so in kawo canji a duniya kuma na fahimci cewa ilimin injiniya shi ne filin da ke magance tasirin matsalolinmu a duniya. Injiniyoyi suna canja duniya ko a yaushe tare da kirkiro mafita da ke shafar rayuwar kowa ta hanyar inganta ta.

Don haka, na samu sake tabbatar da burin zama injiniyar man fetur  da gas a shekarar karshe ta makarantar sakandare lokacin da kusan kowa ke son yin karatun likita. Na tabbata hakan shi ne daidai a gare ni idan na yi la’akari da cewa ina kaunar ilimin sinadarai (Chemistry) da lissafi (Mathematics).

Bayan na fara karanta injiniyanci, sai na fara fahimta da habaka karin sha’awar a cikin kuruciyata lokacin da na fara jami’a. Na san cewa idan ina son in yi nasara a cikin aikin da na yi niyya, dole ne in yi bakin kokarina. Saboda haka, kowane lokacin hutu tun daga shekarata ta biyu na fara zuwa shirye-shiryen horon kwarewa (internship) na wata 2 zuwa 3 don in fahimci bangaren da nake son shiga sosai.

Na kuma yi rajista a matsayin mamba ta Kungiyar Injiniyoyin Man Fetur (Society of Petroleum Engineers SPE) wacce ta taimaka wajen sanya ni in tsunduma cikin ayyukan masana’antar mai da gas. A cikin wadannan shekarun, na hadu da mutane da yawa masu ban mamaki wadanda suka kara min kwarin gwiwa in yi aiki tukuru kuma koyaushe in kasance na yarda da kaina.

 Tarbiyyar da na samu daga iyayena

Mahaifiyata da mahaifina koyaushe sun kasance iyaye na kwarai ababen koyi. Sun yi aiki tukuru don samar da ingantaccen tushe ga rayuwata. Sun koya mini darasi mai muhimmanci game da aiki da aure da mu’amala ta zamantakewa.

Shawarar mahaifiyata da ba zan taba mancewa da ita ba

Abu daya da nake yawan tunawa shi ne a koyaushe tana cewa “Duk inda kika je ko kuma abin da kika taba zama a rayuwar nan, kada ki manta da inda kika fito. Abin da ba za ku iya yi a gabanmu ba, kada ku taba yin sa a bayan idonmu.” Don haka, gaskiya ba ranar da za ta wuce ba tare da wadannan kalmomi su ratsa zuciyata ba.

Kalubale

A koyaushe ina so in ga na yi fice cikin duk abin da nake yi wannan kuwa na nufin dole sai na nuna wani kwazo na daban kafin cimma haka. Sannan ina da matukar sha’awar yin dashe-dashen furanni da girke-girke da  ayyukan kimiyyar kere-kere. A matsayina na daliba a wancan lokaci, ya zama akwai wahala hada karatu da kasuwanci a lokaci guda kamar yadda ba na tsammanin wadansu a gabana sun samu saukin haka. Misali akwai ranakun da ina da muhimmin darasi da ya zama dole in je kuma ga wadansu na bukatar in yi musu girki, hakan ya sa nakan tsinci kaina a halin kaka-ni-ka-yi domin a wannan yanayin za ka ga abubuwa sun cakude mini.

Hakan ya sa kullum ina kokarin in ga na dage da yin ayyukana a lokacin da ya kamata. Wadannan duk su ne kalubalen da

 

na fuskanta.

To amma abin da yake taimakona a cikin irin wadannan ranaku shi ne horo da sha’awar abin da nake yi. Ba na kasala kuma ba na barin aikin makaranta in ce sai daga baya. Ina yin sa a lokacin da ya dace haka kuma harkar kasuwancina. Ina aiki ne game da yin abin da ya dace a lokacin da ya dace.

 

 Inda na fi sha’awar zuwa a lokacin hutu

Ina sha’awar in ga mun je hutu tare da ’yan uwana. Koda a ce kasar waje ce ko a gida ya kasance kowa ya hallara. Sa’annan ina son zuwa Amurka musamman ma birnin New York da kuma kasar Saudiyya.

 

Abin da na fi son yi a lokacin hutu

Ina son yin girke-girke iri-iri. Domin haka ne ya sa na fara sana’ar dafa abinci a kamfain da ake kira TPC Kitchen.

 

Fitacciyar macen da nake sha’awar gani

Ina son wata rana in hadu da Nana Khadija matar Annabi Muhammad (SAW). Domin ina fatar in kwatanta irin so da goyon bayan da ta bai wa mai gidanta (SAW) idan na yi aure. Idan mun hadu zan ce mata da na samu irin halinki da na yi babbar nasara.

 

Burina

Buri na daya a duniya in ga mun rabu da iyayena lafiya. Ina so in ga farin cikin iyayena.

 

Halin da ya fi burge ni ga mata?

Ina son in ga mace mai kamun kai da kare kimarta da mutuncinta.

Tufafin da suka fi burge ni

Abaya.  Duk wanda ya san ni ya san cewa abaya ita ce kayan da nake sawa a kullum. Amma ina sha’awar in ga mace ta saka lafayya duk da dai ni ba ni sawa.

 

Kayan kwalliya

Gaskiya babu kayan kwalliyar da nake so. Saboda ba na kwalliya. Idan ba wani sha’ani da ya kama in je wajen mai kwalliya ta yi mini ba. Kwalliyata ba ta wuce shafa hoda, kwalli da jambaki ba.

 

Turaren da na fi so

Ina son turarurruka da dama amma wanda na fi amfani da shi shi ne ‘flower bomb’ na bictor & rolf.

 

Littafin da na fi sha’awar karantawa

Gaskiya, ni ba mai yawan karatun littattafai ba ne, amma irin littattafan da nakan karanta duk a kan ci gaban mutum ne da kuma karin basira.

 

Abin da nake son a tuna ni da shi

A gaskiya duk inda na je. Ina so in bar shaida mai kyau. Ya kasance a koyaushe akwai abin alheri da za a fada a kaina.

 

Shawara ga matasa musamman mata

Shawarar da zan ba wa mata ita ce a matsayinki na mace, dole ne ki yi aiki sosai, ki yi kokari kuma ki yarda da kanki don cimma burinki. Kada ku bari mutuwar zuciya ta kama ku domin ita ce babbar cikas wurin samun nasara.

Ki fadada ainihin kanki da hankali da kuma horo. Makullin shi ne ki zama ingantacciya, don samun nasara da ci gaba a rayuwarki

 

Shawara ga masu karatu

Shawarar da zan ba yara masu karatu, su yi amfani da damar da ke gabansu. A koyaushe muka samu dama mu yi amfani da ita, yadda ta kamata.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin