✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina son in ga ’yan Arewa sun sake hada kansu – Farfesa Sandra Adamu Pankshin

Farfesa Ladi Sandra Adamu Pankshin ita ce mace ta farko da daga Arewa da ta kai matsayin Farfesar  rediyo da talabijin (Broadcasting). ’Yar Kyaftin Adamun…

Farfesa Ladi Sandra Adamu Pankshin ita ce mace ta farko da daga Arewa da ta kai matsayin Farfesar  rediyo da talabijin (Broadcasting). ’Yar Kyaftin Adamun Pankshin da Mamman ya wake lokacin yana Samanja, malama ce a Sashin Koyar da Aikin Jarida da ke Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta bayyana wa Aminiya tarihinta da alakar mahaifinta da Alhaji Mamman Shata.

Tarihina

Ni ’yar jarumin sojan Najeriyar nan ne da ya yi fice wato Kyaftin Adamun Pankshin na Sashin Sojojin Injiniya. An haife ni a barikin sojoji da ke Yaba a Jihar Legas daga baya kuma aka yi wa mahaifina canjin wurin aiki zuwa Kaduna. Na fara karatun firamare a makarantar ’ya’yan sojoji da ke Barikin Ribadu (Ribadu Cantonment) a Kaduna, na kuma halarci Kwalejin Sarauniya Amina (Kueen Amina) da ke Kaduna. Bayan na kammala kwalejin sai na tafi Kwaleji Koyon Aikin Jarida da ke Ingila. Bayan na kammala karatu a can sai na wuce Los Angeles na kasar Amurka inda na karanta fannin rediyo da talabijin daga nan na tafi Jami’ar Layole Mire Monument a can ne na yi karatun digiri na biyu a Turai da Kolombiya, sai kuma a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya na karanta zamantakewar jarida a sashin nazarin hanyoyin zama lafiya da kawar da rikice -rikicen al’ummomi a inda na samu digiri na uku na Dokta (PhD) kan yadda manema labarai za su gudanar da ayyukansu game da abin da ya shafi rikice-rikice.

Aiki

Na fara aiki ne da Gidan Talabijin na Kasa (NTA) da ke Jos a matsayin Editan Labarai daga nan na koma Kamfanin Jaridar Democrat a Kaduna a matsayin Mataimakiyar Editan Jaridar  Karshen Mako, daga nan kuma na dawo Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya bangaren aikin watsa labarai a matsayin mai koyarwa a sashin Rediyo da Talabijin.

A lokacin da BBC suka zo da kayayyakin watsa labarai suka ba ABU ni aka nema don fannin da na kware ke nan, inda na zama mai shirya yadda za a gudanar da ayyukan tashar na kuma kwashe shekaru goma a kan wannan mukami.

Dama aikin jaridar ba shi ne a zuciyata ba, domin aikin asibitin na so in yi amma muna namu Allah Yana naSa sai wani kawuna ya ce tunda akwai masu aikin jinya a gidanmu da yawa sai ya shawarce ni da in nemi wani fannin. Don haka sai ya ce in shiga karatun koyon aikin jarida domin ya ga irin yawan rubuce rubuce na makaloli da nake yi.

Kalubale 

A gaskiya a bangaren karatu ban fuskanci wasu kalubale ba saboda kasancewa mahaifina ya fara koya mini karatu da rubutu kafin in shiga makaranta a matsayina ta ’yar fari. Ya kuma sanya ni a makarantu masu kyau, sannan da zai tafi yaki ya hada ni da wadansu Turawa ne ina wajen  Turawan ne ya rasu. Daga nan sai na ci gaba zama tare da su. Mahaifina ya fi son in yi karatu duk da bai san cewa ni zan taimaki iyalin ba. Wannan shi ne irin ginshikin karatu da tarbiyyar da na samu wadanda suka kai ni ga wannan matsayi. Ma’anar Sandra ita ce ‘mai taimakon mutane.’

Ra’ayina game da aikin jarida

’Yan jarida su kasance masu fadin gaskiya su cire son rai da neman kudi don karkatar da labaran gaskiya. Kuma su bi ka’i’dodijin aikin jarida, saboda yawancin rikicin da ke aukuwa a tsakanin al’ummomi suna tasowa ne daga irin labaran da ake fitowa da su na rashin gaskiyar abin da ke faruwa.

Yadda ya kamata dan jarida ya zama

Kafin mutum ya bayyana kansa a matsayin dan jarida ya kamata ya tafi makarantar koyon aikin jarida domin ya samu ilimin yadda ake gudanar da ayyukan jarida ba kawai don mutum ya yi karatu a fannin da yake sha’awa ba kuma ba abin da ya hada karatun da karatun aikin jarida sai kawai a rana-tsaka ya ce zai fada aiki jarida. Wannan bai dace ba, kuma shi ne daya daga cikin matsalolin da aikin jarida ke fuskanta a Najeriya.

Mutanen da  suna da gaskiya, suna da natsuwa wajen gudanar da aikin, amma yanzu abubuwa na jan hankalin matasa ba su sa zuciyarsu a wuri daya domin su fahimci aikin yadda yake.

Mahaifina da alakarsa da Shata

Adamun Pankshin ya shiga aikin soja a lokacin Turawan Birtaniya a 1947. Ya fara daga kurtu a bangaren S&T na Rundunar Sojan Najeriya. Dogo ne kuma kakkarfa, wata rana yana cikin aiki a wurin aikinsu sai wani Bature ya gan shi, ba tare a bata lokaci ba sai ya ce bai kamata a bar shi a wannan wuri ba, sai ya bayar da umarni a kai shi bangaren injiniyoyi a 1953. A lokacin da Turawa za su bar Najeriya sai aka tura shi kasar Ghana don karo ilimi a fannin aikin Injiniya.

Ya shiga aikin soja da iliminsa ba kamar wadansu da suka shiga aikin sojan ba ilimi ba. Kafin Turawa su tafi sai aka ba mahaifina mukamin Samanja mukamin da shi ne dan Najeriya na farko da ya fara rikewa a fannin sojojin injiniya, kuma shi ne RSM dan Najeriya na farko. Daga nan ne sai aka fara Yakin Basasa, kuma saboda kwazo da kwarewarsa ce kafin rasuwarsa aka yi masa karin girma inda ya samu anini uku (Kyaftin) saboda yadda ya jajirce ya kama garuruwa da dama a lokacin Yakin Basasa.

Mahaifina da Alhaji Mamman Shata abokai ne, lokacin da Shata ya zo Jos yin wasa ne suka fara haduwa har suka tafi farauta tare. Sannan Alhaji Mamman Shata yana binsa wajen yaki a wancan lokaci ana ba shi Bataliya da kudi don biyan dakarunsa hakkokinsu.

Kuma yakan gayyaci Shata don ya nishadantar da sojoji bayan gwagwarmayar yaki da suka kammala, dukkan wakokin da Shata ya yi wa mahaifina abin da ya gani ne ba labari ake ba shi ba. Wani abin sha’awa da Shata ba ya yin waka ga mutum don kudinsa sai dai ra’ayi da kauna.

Alakata da Shata 

Muna da kyakkawar alaka da marigayi Mamman Shata kwarai da gaske domin muna zama da shi mu yi hira kafin ya rasu, kuma yana ba ni tarihin wasu abubuwa da ban sani ba, kamar yadda Shata ya ba ni labarin harkar farauta sai jan namiji mai juriya. Kuma a cikin wakokin Shata wakar Adamun Pankshin tana daga cikin na farko-farko da ake jinsu kuma tana cikin na goman farko a wakokin Shata. A lokacin da Shata ya yi masa wakar yana da mukamin Saja Manjo ne (Samanja), amma ya bar aikin soja da anini uku yana Kyaftin.

A lokacin da nake a gidan talabijin na Jos duk lokacin da Shata ya shigo garin Jos sai ya zo ya gan ni don mu gaisa kuma ya nuna min so sosai kamar yadda ya so mahaifina, akwai abokantaka a tsakanin iyalinmu da na Shata.

Alhaji Mamman Shata ya gaya mini cewa a ranar da ya fara haduwa da Adamun Pankshin fada suka yi, amma bai gaya mini dalilin fadansu ba. Sai dai tun daga wannan lokaci suka zama abokai bayan da suka fahimci kansu,  abin da Shata ya gaya mini ke nan.

Burina

Burina a samu hadin kai a Arewacin Najeriya. Domin tafiyar wannan zamani a gaskiya babu kyau, Arewa da kanmu daya, komai namu daya amma yanzu mun rarrabu. ’Yan siyasa ne suka raba domin sai ka ji sun ce kana hulda da wannan mutum da ba Musulmi ba ko ba Bahaushe ba Ko kuma sai ka ji an ce daga wane bangare ya fito? Wannan ya ba ’yan siyasa damar nuna mana bambancin da ke tsakaninmu sabanin a baya da a Ranar Sallah mu ci tuwon Sallah, Ranar Kirsimeti ku ci tuwonmu. Amma yanzu babu yarda a tsakaninmu hakan ya faru ne domin neman kuri’ar jama’a.

Shugabannin wannan lokaci ba kamar na baya irin su Firimiyan Arewa Sardauna  Sa Ahmadu Bello ba ne, a gidansa akwai kusan mutum 100 daga addinai daban- daban da kabilu daban-daban, amma in ba an gaya maka ba, sam ba za ka taba ganewa ba. To ya kamata a ce mu koma kamar yadda muke a da kafin rarrabuwar kawuna ta shige mu. Mu kuma yarda da juna in kuma ba mu yarda da juna ba, to ko shakka babu lamarin ba zai yi kyau ba. Misali a Yakin Basasa an tsara yadda za a gama da Hausawan Arewa sai ’yan Middle Belt suka ki yarda suka hada kai da Hausawan Arewa. To yanzu ma lallai ne mu hada kai saboda in wani yakin ya taso shiyyar da ke da mafi yawan sojoji ba za su taimaka wa wani bangaren ba. Domin haka ya kamata mu gyara zamanmu da gaskiya mu so juna mu yi harkokinmu tare kamar da. Ni na yi imani cewa Arewa daya ce, domin yadda mahaifina ya zauna da Hausawa ya shaku da su.

Yadda nake yin hutu 

Na fi son karanta labarai amma ni ba ni da sha’wa ga kallon wasan kwaikwayo. Ina karanta jaridar Aminiya kuma ina yaba mata ganin yadda suka ba mata muhimmanci kwarai da gaske ta fitar musu da shafi na musamman a kan rayuwarsu. Abin da na dade ina karantawa sai ga shi yau kuma da ni ake tattaunawa. Don haka ina ba su shawara su daure domin shi aikin wayar da kan al’umma da fahimtar da su abu ne mai wahala kwarai. Allah Ya taimake ku a kan aikinku na gode.

Shawara ga ’yan jarida

A gaskiya duk wanda ke aikin jarida ya kamata ya rika zuwa karo ilimi don inganta aikinsa, lura da sababbin tsare-tsare da yanayin kayan aikin da sanin makaman aikin a halin da ake ciki na zamani. Kuma ’yan jarida su daina raba kawunan mutane ta wajen rubuce-rubucen kin jinin juna da suke hadasaa yake-yake a tsakanin al’umma.

Shawara ga mata

Iyaye su goyi bayan ’ya’ya mata su yi karatu, su karfafa musu gwiwar ci gaba da karatu har zuwa jami’a, kuma maza su bar su, su yi aiki domin su ci gaba, al’umma su amfana da baiwar da Allah Ya yi musu, kasa da Arewa su ci gaba.