Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ina son in zama babban jarumi a Kannywood – Yusuf Saseen

Matashin Jarumin Fina-Finan Hausa, Yusuf Muhammad Abdullahi wanda aka fi sani da suna Sasen, ya bayyana wa Aminiya tarihinsa da matakin da yake son takawa a wannan masana’anta ta Kannywood

Tarihina

ADVERTISEMENT

Sunana Yusuf Muhammad Abdullahi wanda aka fi sani da Saseen. An  haife ni a birnin Kano, na yi makarantar firamare ta Makama da ke Karamar Hukumar Birni. Daga nan  na tafi Karamar Sakandare ta Sabuwar Kofa bayan na kammala sai na wuce Babbar Sakandare ta Rumfa daga nan sai na wuce Jami’ar Bayero, inda na yi Difloma a kan kula da laifuffuka (Crime Management). Daga baya na sake koma wa Jihar Binuwai;  na yi karatun Difloma a kan kasuwanci a Kwalejin Sana’a da Fasaha ta garin Gboko. Bayan na kammala sai na wuce Jamhuriyyar Benin; na yi digiri a kan Kasuwanci a Jami’ar Sainte Felicite da ke garin Porto Nobo.

Yaushe ka fara harkar fim?

ADVERTISEMENT

Na fara shiga harkar fim ne a watan Nuwamban shekarar 2017, amma tun ina yaro ina sha’awar in ga na zama dan fim saboda yana daya daga cikin sana’o’in da ke mayar da dan talaka sarki kuma hanya ce da mutum zai nemi halalinsa a sauwake.

Wane fim ka fara fitowa, kuma wane ne ya bayar da umarni a fim din?

Fim din da na fara fitowa a ciki shi ne fim din ‘CIKI DA MAGANA’ wanda fim din Ibrahim Birniwa ne. Amma sai dai fita ce ta musamman na yi a cikinsa saboda a karshe na fita ne a waka. Sanusi Oscar ne ya bayar da umarni.  Fim din da na san na yi kuma da na fara fita sosai shi ne fim din ‘CAMFI’ wanda shi kuma fim din Nazifi Asnanic ne kuma Ibrahim Bala ne ya ba da umarni a cikinsa wanda kuma ya dauki nauyi shi ne Sani Mai Iyali, sai kuma fim din HUMAIRA.

Ban da wadannan fina-finai ko akwai wasu da ka taba yi?

Eh, na yi akalla ya kai Fim 20. Akwai wadanda suka fito akwai wadanda ba su fito ba. A  cikin wadanda suka fito akwai  Camfi da Wa Nake So, da Auren Kaddara, sai kuma  jerin fim din Arewa 24 (Series) na Kwana Casa’in, wanda a ciknsa na fito M.D Faruk. Sannan akwai wanda na yi na Series; amma bai  fito  ba tukuna yana kan hanya. Labarin Aminu Saira ne kuma shi ne ya bayar da umarni a ciki, kusan duk lokaci daya na yi shi da Camfi.

Wane mataki kake son kaiwa a cikin wannan sana’a ta fim?

Ina son ganin na taka matakai da yawa, amma a gaskiya ina son in ga na taka wani matsayi babba a cikin wannan sana’a ta yadda ni ma zan samu damar ba da tawa gudunmawa ta alheri wadda za ta amfani al’umma gaba daya.

Wadanne kalubale kake ganin Masana’antar Kannywood take fuskanta?

Masana’antar tana fama da kalubale da yawa amma dai wanda ya fi fitowa fili shi ne rashin hadin kai da hangen nesa.

Wace shawara gare ka ga abokan sana’a ganin yadda ake ta samun rashin jituwa a tsakanin manyan jarumai daga cikinsu?

Akwai rashin shugabanci, ya kamata a samu jarumtattun shugabanni da ba su da son zuciya.

Ko akwai wani kira da za ka yi wa gwamnati don shigowa cikin harkar fim?

Ya dace gwamnati ta shigo cikin lamuran masu fim a dama sosai da ita. Domin ita kadai ce za ta iya ba mu kariya tare da saita mu a kan al’adunmu da addininmu da kuma irin sakonnin da muke aikawa zuwa ga al’umma.

Wani jigo daga cikin Kannywood ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya bai wa ’yan fim mukamin minista lura da irin gudunmawar da suka bayar a zabubbukan da suka gabata ko kana goyon bayan haka?

Ina goyon baya sosai saboda wannan shi ne zai kara kawo mana hadin kai tare da inganta sana’ar tamu ta zama ta samu kima a duk duniya.

Ko kana da wani sako zuwa ga masoyanka?

Masoyana ina godiya a gare ku kuma ina rokonku da ku ci gaba da yi mana addu’a Allah Ya kara saita mu a kan hanya madaidaiciya.