✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina za mu a Nes Lebul? (5)

Domin a sanya takunkumi a bakunan wadannan ’yan adawa sai aka shiga soke rajistar kungiyoyin da suke tattaruwa kansu, wadansu aka sa su yin hijirar…

Domin a sanya takunkumi a bakunan wadannan ’yan adawa sai aka shiga soke rajistar kungiyoyin da suke tattaruwa kansu, wadansu aka sa su yin hijirar dole, wadansu aka hana jama’a hulda da su, wadansu aka hana su amfani da kayan gwamnati wajen tarurrukansu. Irin wannan kisan mummuke shi Sarkin Bauchi Adamu ya yi amfani da shi wajen soke Kungiyar Ci Gaban Jama’ar Bauchi. Bai dai ce kada a ci gaba da gudanar da kungiyar ba, amma da ji an san manufarsa. Ya ce da Sa’adu Zungur da su Malam Aminu Kano da ke gudanar da harkokin kungiyar, “Ba wanda ya ce kada ku yi tarurrukanku na kungiya, sai dai abin da ba ya bisa ka’ida shi ne ku yi amfani da kayan gwamnati ko kuma ku yi amfani da lokacin aikin gwamnati domin gudanar da tarurrukanku.” Ta haka aka bi aka rika jefa ko aza shingaye gaban ’yan adawa, wanda kuma shi ya haifar da abin da yau aka gani na tashin-tashina a fagen siyasar Arewacin Najeriya har zuwa yanzu.

Kila tambayar da wadansu za su yi a nan ita ce, me ya sa aka rika samun shan-daga a tsakanin wadansu daga cikin al’ummar Arewa da kuma ’yan mulkin mallaka da danniya da hukumomin En’e-En’e da sarakuna? Amsar ita ce tun kafin Jihadin Usman Dan Fodiyo, da ma lokacin jihadin da bayan kammala jihadin, an sha samun mutane daga Arewa da ba su ganin jinjiri a bayan mahaifiyarsa ba su tambayi wane ne mahaifinsa ba. Ma’ana, an samu mutane da suke kyamar zalunci da cin zali da handama da babakere da kuma musguna wa wasu sassa na al’umma. A kullum irin wadannan mutane sukan tari gaba su hana aukuwar irin wannan ta’asa, wadansu har ransu suke mikawa don kare al’ummarsu.

Daga cikin irin wadannan mutane an samu labarin su Bakin Wake a yankin Katsina (kafin jihadi) da Malaman ’Yandoto (zamanin masu jihadi) da Malaman Satiru (zamanin zuwan Turawan mulkin mallaka). Sai dai Yakin Duniya na Biyu ya kara bude idanun mutanen Arewa dangane da yadda duniya take ciki. Sojojin da suka halarci fagen-fama a wasu sassa na duniya sun dawo gida da tunanin lallai ’yanci na da dadi, saboda haka tare da taimakon ’yan siyasa da suka yi karatu mai zurfi game da gina kasa da tattalin arziki, sai aka shiga zafafa tunani da tattauna matsaloli da kuma bijere wa duk wasu abubuwan zalunci da danniya, wanda hakan ya kawo ka-ce-na-ce da tashin-tashina a tsakanin masu mulki da sauran ‘talakawa.’

Ba wani abu da ya kara tunzura ’yan adawa wajen bijire wa duk wani tanadi da hukumomin Turawa suka yi tare da agajin sarakuna, sai irin yadda aka mayar da ’yan adawa tamkar ba mutane ba. An tafka ayyukan assha ga ’yan adawa, ba a kuma tsaya ga soke rajistar kungiyoyinsu ba, an hada da kame da daurin karya da bugu da kisan kai, irin wannan ne ya sa a can Hadeja ake yi wa alkalin garin kirari da cewa Alminjir ne maganin ’yan NEPU, mai daure mai gaskiya don marar gaskiya ya ji tsoro.

Ke nan ba bisa tsarin doka da gaskiya ake dauri da musgunawar ba, an yi amfani da kotu da alkalai da ’yan doka aka rika kuntata wa ’yan adawa, su kuma sarakai sun sa ido, wata sa’a ma suke azabtarwar, su kuma ’yan mulkin mallaka na jin dadin yin haka. Alal misali su Illa Ringim da Danjani Hadeja da wai aka kama su da laifi, daure kafafunsu aka yi a jikin dawakai ’yan Azbin, aka sa bulala aka rika bugun dawakan nan, suka rika jan su a kasa, tun daga Sabon Garin Mai ’Ya’Ya har cikin birnin Kano, ba don komai ba, sai don sun halarci taron siyasa ba tare da famit ba.

Wadansu kuwa daga cikin ’yan adawar, an yi musu yadda aka yi wa Musulmin farko ne a Makka, wato aka matsa musu sai sun yi riddar siyasa daga NEPU zuwa NPC, musamman wadanda aka kai gaban Sarkin Kano Sanusi domin yi musu shari’a ko hukunci. Irin wannan tursasawa ce ta sa ’yan adawa da dama suka gwammace su je gaban kotunan Turawan mulkin mallaka, maimakon Kotunan Shari’a (alkalai) idan an ba su zabi a lokacin da ake tuhumarsu. A gaban alkalin Sarki ba a tambayar bahasi, ba beli, sai dai dauri kawai ga ’yan NEPU ko ’yan adawa.

Ba wannan kadai ba, a can kauyuka akan matsa wa talakawa su bayar da hatsin kambi. Wadansu magidanta kuwa an sa su dole su gina shararra ne daidai inda gidajensu suke, daga wannan kauye zuwa wancan ta amfani da kayan abincinsu, dogarai na biye, suna zagayawa, suna yi wa malalaci bulala, in ya nemi ya huta, wanda ya nemi ya yi tsiwa ko rashin kunya nan take za su buge, su daure domin su aikinsu bai wuce hushi da hushin wani ba. Haka kuma ga bala’in nan na noman Gandun Sarki, ga biyan kudin ushira (gado), ga kwana da matan talaka ko ’yan adawa a duk lokacin da dagaci ko hakimi ya kai ziyara wasu sassa na kasarsa, ko kuma a yi shela a kai amarya gidan uban kasa kafin a kai ta dakin mijinta.

Daga 1954, lokacin da NPC ta soma mulki a Arewa, ’yan adawa ba su ji dadi ba, Lawal Dambazau wanda yana raye a lokacin ya jaddada haka, inda yake cewa, daga wannan shekara Jam’iyyar NPC ta shiga yaki da talakawa, duk wanda ya ki goya wa jam’iyyar baya sai ka ga an cinno masa sarakuna ko alkalai ko ’yan doka su yi masa yaga-yaga. Su kuma malamai da daliban addini tuni aka yi musu nuni da cewa ai Jam’iyyar NPC, jam’iyya ce ta Shehu Usman Dan Fodiyo, don haka su ’yan NEPU da magoya bayan su duk kafirai ne, abin yaka. A yawancin lokuta an sha kai hari gari (don kame) ga ’yan adawa, kamar yadda ake harin bayi, wadansu a kai gidan yari, wadansu a yi musu dukan tsiya, wadansu a washe musu gidaje, wasu a lalata sana’arsu ko kayan sana’a, kamar gonaki, wadansu a kwace musu mata, wadansu su ma rasa rayukansu.

Za mu ci gaba