✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina za mu a Nes Lebul? (6)

Ganin irin wannan rayuwa ta kunci da tashin hankali da talakawa ko kuma ’yan adawa suka shiga, ya sa wadanda aka kai ga bango sukan…

Ganin irin wannan rayuwa ta kunci da tashin hankali da talakawa ko kuma ’yan adawa suka shiga, ya sa wadanda aka kai ga bango sukan yi kukan kura, sukan nemi mafita ta kowace irin hanya. Tunda yake talakawan ba su da goyon bayan hukuma, ba su da alkalai ko ’yan doka, sai yawancin ’yan adawa suka shiga mayar da martani ta hanyar da suka san hukuma ba za ta iya hanawa ba. Da farko dai suka kulla kawance da Jam’iyyar NCNC ta Azikiwe, wadda a wancan lokaci tana da jaridu masu yawan gaske da take amfani da su wajen fafatawa da ’yan mulkin mallaka da masu goya musu baya.

A daidai wannan lokaci akwai jaridu da suka yi tashe irin su Gaskiya Ta Fi Kwabo, wadda take ta hukuma ce da aka kafa domin farfaganda. Tun daga shekarar 1954 kuma Gwamnatin Arewa ta sake samar da jaridu na larduna, ta yadda zuwa shekarar 1956, kusan kowane lardi na da tasa jaridar, kai har inda ma ba a amfani da harshen Hausa an kafa musu tasu. A Lardin Kano, inda nan ne hedikwata ko mazaunin NEPU da yawancin ’yan adawa, jaridar Sodangi da Daily Mail su ne tambarin NPC wajen farfaganda. Ta amfani da wadannan jaridu hukumar mulkin mallaka da Jam’iyyar NPC suka shiga yada karya game da NEPU da magoya bayan jam’iyyar. Sa’annan hukuma ta tabbatar da ba a ba ’yan adawa damar amfani da jaridun ba, balle a ji ta bakinsu. Duk wani aikin ci gaba ko wani abu da hukuma ta san zai sa NEPU ta samu tagomashi ko goyon baya, to ba a sa shi a cikin jaridun Sodangi da Daily Mail.

Dangane da haka abin da Jam’iyyar NEPU ta fara nema daga kawancenta da NCNC shi ne a sama musu wurin da za su rika mai da martani game da farfagandar hukuma da Jam’iyyar NPC. Wannan ya sa aka samar da jaridar Daily Comet a Kano, aka kebe wani bangaren jaridar domin dimbin masu karatun Hausa. An yi haka ne domin an riga an san cewa farfaganda ta fi armashi a cikin harshen da mutane ke fahimta. Kafuwar Daily Comet a Kano sai rawa ta canja, wanda a da yake kan doki, sai ya koma kan kuturi, wannan ya bayar da dama aka shigo da bayanan da ba su da dadin ji ko saurare, bayanai na batunci da cin mutunci da yarfe da zagi ga tagwaitattun al’ummar Arewa.

A cikin jaridar Daily Comet, ta ’yan adawa, musamman a shafukanta na Hausa, aka shiga fallasa da yin zambo da zagi game da ayyukan assha na gwamnatin ’yan mulkin mallaka da hukumomin En’e-En’e da sarakuna da lalatattun manufofin Jam’iyyar NPC, musamman lokacin da zabe ya doso a shekarun 1956. ’Yan adawa sun yi amfani da wannan dama wajen mayar da zagi da fallasa NPC, suka shiga yayatawa da daga Jam’iyyar NEPU da manufofinta. A wancan lokaci ba wai magana ce ta fadar gaskiya ba, harka ce ta farfaganda, neman suna da nuna iya adawa. Wannan shi ya kara haifar da siyasar jan-daga a tsakanin jam’iyyun biyu, adawa ta koma ‘yaki’, kunya ta kau, sai tsageranci ya zama abin ado, ba wai manufofin jam’iyyun ba. Zagi da cin mutuncin shugabanni na siyasa ko mulkin mallaka ko kuma sarakai da hakimai da dagatai ya zama ruwan dare.

Daga wannan lokacin sai abubuwa suka sake rincabewa, kamfen ko yakin neman kuri’a na sanin ya kamata da amfani da manufofin jam’iyya, tuni aka yi watsi da su, musamman ma a wajen ’yan adawa da suka sha zagi da tsinuwa da dauri da kisa na wani lokaci mai tsawo, kuma aka hana su su koka. Saboda haka duk abin da ya fito daga wajen ’yan NEPU, a wajen yakin neman zabe ne, a cikin jaridu ne ko a wake ne, za a a iske shi cike yake da zagi da zambo da habaici da zambo-zagi.

Wannan ne ya sa jagororin jam’iyyun biyu da sauran shugabanni, suka shiga uku a tsakanin magoya bayansu. Shugabanni irin su Aminu Kano da Gambo Hawaja da Illa Ringim da Danjani Hadeja (a NEPU), sai kuma irin su Sardauna da Koguna da Sarkin Kano Sanusi (a NPC), sun sha zagi da batanci. Kalamai irin su ‘jakai’ da ‘marasa kaciya’ da ’yan daudu’ da ‘dan makahon birni’ da ‘jahili’ ko ‘wawa’ ko ‘banzan-bazara’ ko ‘sususu’ aka rika musaya tsakani domin nuna goyon baya ko akasin haka.

Wani abu da ya fito karara shi ne dukkan jam’iyyun biyu suna ikirari da cewa su ne Musulmi, haka kuma manyan darikun nan guda biyu na Tijjaniya da Kadiriyya, sun rarrabu wajen goya wa jam’iyyun baya. Da yake kuma akwai malamai da masana a tsakaninsu, sun sha amfani da addinin domin samun galaba. Alal misali a lokacin da Jam’iyyar NPC ke kiran kanta da jam’iyyar Shehu Dan Fodiyo, shugabanta kuma jikan Dan Fodiyo, wanda ya kamata a goya wa baya, domin shi ‘bin na gaba ai bin Allah ne’ sai abin ya koma ga habaici da jefa magana. Irin su Danjani Hadeja, sun yi ikirarin cewa ai su wadanda Allah Ya ce a bi su, su ne wadanda za su yi umarni ga kyakkyawan aiki, su yi hani ga barin mummunan aiki, ba cewa ake yi a bi Sarki ko Koguna ko Sardauna kurum ba, sai in za su yi umarni a bi dukkan abin da Allah Ya ce a yi. Danjani Hadeja kan ce ko ana nufin mu bi malamai, su su bi Sarki da Sardauna, su kuma Sarki da Sardauna, su bi Turawa?

Danjani Hadeja yakan yi nuni da cewa ’yan Jam’iyyar NPC suna amfani da Musulunci ne kurum don ci da addini, yana karawa da cewa,ba inda a cikin Shari’ar Musulunci aka ce a nuna bambanci, ba inda aka ce a ba da kudi don neman galaba, ba inda aka ce a girmama Sardauna a wulakanta gyartai. In kuwa akwai, ya ce sai a gaya masa ayar da ta ce a yi kukan masallaci na karya don jin dadin Sardauna da jam’iyyarsa. Kuma wace aya ce ta ce wadansu sarakuna su sayi motoci da kudin talakawa?’

Fahimtar abin da zai sa wani ya yi irin wannan zargi da batanci ga shugabanni zai samu ne kurum ta nakaltar yadda abin ya samo asali, ya kuma kasance ne kamar yadda muka nuna daga irin dangantakar da ke tsakanin gwamnatin mulkin mallaka da hukumomin En’e-En’e da sarakuna da ’yan tagajan gari. Shi yaki ko tashin-tashina irin na siyasa ba na rago ko matsoraci ba ne, don haka abin da ’yan adawa ke takama da shi bai wuce batun nan ba da Hausawa ke cewa ‘an ga kabarin mai kuru, amma ba a ga na matsoraci ba’. Shi ya sa ’yan adawa ba su ji tsoron rama cuta ga macuci ba, ba su ja da baya ba.

 

Mun kammala