Daily Trust Aminiya - Indiya ta harba kumbonta zuwa duniyar Mars
Subscribe

Indiya ta harba kumbonta zuwa duniyar Mars

 Rokar Indiya da aka harba duniyar MarsIndiya ta harba kumbonta zuwa duniyar Mars, a kokarinta na harba tauraron dan Adam a kan falakin wannan duniya, tare da dabarar karanta yawan kudin da aka kashe a ayyukan harba kumbo sararin samaniya da ta gudanar a baya; kuma wannan al’amari ya sanya kasar cikin jerin kasashen yankin Asiya da ke kashe dimbin kudi a harkar sararin samaniya.

An harba kumbon zuwa falakin duniyar Mars daga gabar kogin Kudu maso Gabashin Indiya, dama tuni a aka harba tauraron dan Adam wanda ke laluben sinadarin Methane da ma’adinai. “Wannan shi ne farkon yunkurinmu na shiga duniyoyin sararin samaniya,” a cewar Mista Debiprasad Karnik, mai amgana da yawun Cibiyar Binciken Sararin Samaniya ta Indiya (ISRO).
kasashe uku hne kawai suka bayar da shaidar da ta gamsar cewa sun taba aike wa da kumbunan da suka sauka a duniyar Mars. Wadannan kasashe sun hada da Amurka da Turai da Rasha. Yunkurin shiga duniyar Mars ya sha cin tura, musamman ma ganin yadda kasar Sin ta kasa kaiwa ga wannan duniya, yayin da ta harba kumbonta daga falakin wannan duniyar (da muke ciki) a shekarar 2011.

texem
More Stories