✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Indiya: Zakzaky da Gwamnati sun sake sa zare

Ko Kiriqiri bai kan nan tsaro ba – Zakzaky Zakzaky na son zama a babban otel ne – Gwamnati Shugaban Kungiyar Harkar Musulunci (IMN) ta…

  • Ko Kiriqiri bai kan nan tsaro ba – Zakzaky
  • Zakzaky na son zama a babban otel ne – Gwamnati

Shugaban Kungiyar Harkar Musulunci (IMN) ta mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky ya nuna rashin gamsuwarsa da asibitin da aka kai shi a Indiya, musamman kan yadda ake kula da shi.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta ce a yi watsi da maganarsa yana so ne kawai ya kawo rudu a lamarin.

A wani sakon murya da ya fitar, Sheikh Zakzaky ya ce, “Mun fahimci cewa sun kawo mu ne, sannan aka fara lura da mu ba yadda aka tsara ba. Domin a tsarin da muka shiga kafin mu zo, an ce likitocin da muka zaba ne za su duba mu. Sai likitocin suke fada mana cewa ba a bar su su duba mu ba. Don haka mu ma ba za mu bar likitocin da ba mu sani ba su duba mu. Ba zai yiwu ba mu bar su su samu abin da suka kasa samu da bindiga. Don haka a takaice ba mu yarda da tsarin ba. Kawai sun kawo mu nan ne su tsare mu.”

“An taba tsare ni na shekara 13, amma ban taba ganin irin wannan tsarewar ba domin ko dakin da nake ciki akwai ’yan sanda rike da bindigogi suna tsare ni, kuma ba ni da damar fita zuwa wani dakin. Ko da nake tsare a gidan yari, ana bari mu fita bayan karfe 7 na safe. Ko Kirikiri bai kai wannan ba. Don haka ne nake cewa ba zai yiwu mu bar wannan wajen tsaremu ba a Najeriya, sannan mu dawo nan a ci gaba da tsare mu. Don haka abin da ya fi dacewa shi ne mu koma gida kawai sai mu nemi wani asibitin a wata kasa. Yanzu haka kasashe irin su Malesiya da Turkiyya da Indonesiya sun nuna amincewarsu mu je can a yi mana magani,” inji Zakzaky.

Da take mayar da martani game da zargin da Sheikh Zakzaky ya yi cewa ana takura masa a kasar Indiya, Gwamnatin Najeriya ta ce malamin ne ya so ya kauce wa ka’aidojin tafiyarsa.

A wata sanarwar da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Watsa Labarai da Al’adu, Misis Grace Isu Gekpe ta sanya wa hannu, ta ce “Ya kamata a yi watsi da ikirarin da Sheikh Zakzaky ke yi cewa ana tsare da shi a yanayin mai muni fiye da yadda yake tsare a Najeriya.”

Sanarwar ta ce Shugaban na IMN din ne ya nemi a ba shi wasu dama wadanda aka hana domin ba su cikin tsarin tafiyar.

Wadannan abubuwa kuwa sun hada da barin likitoci wadanda shi ne kawai ya amince da su su duba shi, da mika masa fasfo dinsa a lokacin da suka isa Dubai da ba shi damar zama a otel maimakon asibiti da kuma bukatar a janye ’yan sandan da ke tsaronsa a kasar Indiya.

Zargin da malamin ya yi a cikin muryar ya janyo hankalin mabiyansa, inda suka yi zargin cewa da hadin bakin gwamnatin Najeriya ne ake takura wa malaminsu.

A wata hira da BBC, ’yar Sheikh Zakzaky mai suna Suhaila ta tabbatar da cewa mahaifinta ya koka game da yanayin da ake tsare da shi a kasar Indiya.

A ranar 12 ga watan Agusta ne Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenat suka tafi Indiya don neman magani, bayan kwashe shekaru ana tsare da su.

Tsarewar da Gwamnatin Najeriya ta yi masa ta janyo jerin zanga-zanga daga magoya bayansa, abin da ya haifar da rasa rayuka.

A ranar 5 ga watan Agusta ne wata Babbar Kotu da ke Kaduna ta bai wa Sheikh Zakzaky damar zuwa neman magani a wani asibitin kasar Indiya, bayan kai-ruwa rana da aka yi ta yi a kotu a wata shari’a da ake yi tsakaninsa da Gwamnatin Jihar Kaduna.