✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC na shirin fara zabe ta intanet a 2021

INEC za ta ci gaba da yi wa masu zabe rajista a watannin farkon shekarar 2021.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ce za ta ci gaba da yin rajistar masu zabe a farko na shekarar 2021.

Hukumar kan yi wa mutane rijista a duk shekara ne domin bai wa wadanda suka kai shekarA 18 ko ba su taba yi ba damar fara kada kuri’a.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu bayan ya kare kasafin kudin hukumar na 2021 a Majalisar Tarayya ya ce, “Za mu dauki shekara daya da rabi muna yi, har zuwa saura wata shida kafin babban zaben 2023”.

Ya ce, a yanzu haka hukumar ta na fuskantar shari’o’i 1,700 da aka shigar kanta game da zaben 2019.

“Kullum zaka jin mutane na kai kara kotu suna saka sunan INEC a ciki,” inji shi.

Da yake kare kasafin kudin, Yakubu ya ce INEC na son ba ‘yan Najeriya mazauna ketare damar yin zabe a inda suke ta hanya kimiya, amma sai an yi kwaskwarima ga dokar zabe.

A wata tattaunawa, shugaban hukumar ya bayyana yiwuwar amfani da na’urar kada kuri’a ta laturoni a zaben Gwamnan Jihar Anambra da za a yi a babi.

Ya shaida wa Majalisar cewa hukumarsa na kokarin cimma matsaya kan zabe ta intanet wanda ya ce sama da kamfononi 40 suka muna kwarewarsu a kai.

“Sun nuna mana za su iya, abun da ya rage shi ne hukumar da samu matsaya. Amma ba za mu iya cewa nawa za a kashe ba ko kuma ranar da za fara.

“Muna dai yin bakin kokarinmu, za mu kawo injinan zaben, mu jaraba a zaben gwamnan Jihar Anambra a shekara mai zuwa”, inji shi.

Shugabar Kwamitin, Majalisar kan INEC, Aishatu Dukku, ta ce za su yi duk abin da ya dace domin tabbatar da cewa hukumar da aiwatar da kudirinta.