✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta karbe shaidar cin zabe ’yan takara 64 a Zamfara

Shugaban Hukumar zabe ta kasa INEC Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce hukumar ta karbe takardar shaidar nasarar cin zaben, wato Certificate of Return, na ‘yan…

Shugaban Hukumar zabe ta kasa INEC Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce hukumar ta karbe takardar shaidar nasarar cin zaben, wato Certificate of Return, na ‘yan takara 64 da ta bai wa ‘yan takara da suka yi nasara a zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a jihar Zamfara.

Shugaban INEC din ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin da yake mika takardar shaida ga zababben gwamnan jihar da mataimakinsa da sauran ‘yan majalisar dokokin jihar.

Wannan ya biyo bayan wani umarni ne da hukumar ta ce ta samu daga wata kotu a birnin Sakkwato game da rikicin jam’iyyar APC da ke da alaka yadda aka yi zaben fitar da gwanin da suka yi mata takara a jihar.