Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Infantino ya yi ta-zarce a shugabancin FIFA

Infantino ya yi ta-zarce a shugabancin FIFA

A shekaranjiya Laraba ne aka sake zabar shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino a karo na biyu.

Infantino dai ya sake zama shugaban hukumar ne ba tare da hamayya ba, ma’ana babu wanda ya yi takara da shi.

A 2016 ne ya gaji tsohon shugaban hukumar Sepp Blatter wanda ya shafe lokaci mai tsawo amma ya yi murabus saboda zargin badakalar cin hanci da rashawa da ta dabaibaye wasu jami’an hukumar a wancan lokaci.

Infantino dai ya yi alkawarin zai kara yawan kasashen da ke halartar gasar cin kofin duniya daga 32 zuwa 48 da hakan ya janyo cece-ku-ce.

Yanzu dai wa’adin mulkinsa na biyu zai kare ne a 2023.