✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Inganta magungunan gargajiya na iya samar da saukin kiwon lafiya – Bunkau

Wani kwararren mai ba da magungunan Musulunci da na gargajiya, Dokta Adam Ahmad Bunkau, ya ce ingatattun hanyoyin ba da magungunan gargajiya suna iya samar…

Wani kwararren mai ba da magungunan Musulunci da na gargajiya, Dokta Adam Ahmad Bunkau, ya ce ingatattun hanyoyin ba da magungunan gargajiya suna iya samar da saukin ga kiwon lafiya ga ’yan Najeriya.

Likitan wanda shi ne Shugaban Cibiyar Maganin Gargajiya ta Bunkau Traditional Medicine and Clinic ya bayyana haka ne a cibiyar da ke hanyar Keffi a Jihar Nasarawa.

Ya ce asibitin bada maganin gargajiyar wanda aka gina a bara, an samar da  shi ne saboda bada magungunan gargajiya da na Musulunci a bangarori da dama, inda ya ce yafi bada karfi a kan inganta garkuwan jiki.

“An horar da mu wajen ba da muhimmanci a kan garkuwar jiki maimakon ciwo. Idan aka inganta garkuwar za ta kare kanta daga cututtuka saboda mun gano cewa garkuwar jiki ita ce ginshikin dan Adam wadda karfinta ke tabbatar da lafiyar mutum,” inji shi..

Da yake bayani kan ayyukan cibiyar, ya ce, ya samu horarwa daga kwararru a kasashen Jordan da China., inda ya ce magungunan gargajiya suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen takaita yaduwan cututtuka a tsakanin ’yan Najeriya.

Ya bukaci al’umma su rika cin abincin da jikinsu ya fi bukata maimakon wanda bakunansu suke bukata.  “A kullum muna bai wa marasa lafiya da sauran jama’a shawarar cewa su dage da cin abin da zai inganta lafiyar jikinsu fiye da abubuwan da bakunansu suka fi so Yawancin marasa lafiya da suka rungumi shawarwari da magungunanmu suna ba da shaida mai kyau a kai. Mutane sukan kira mu daga kasashen waje su nemi bayani a kan yadda muke gudanar da ayyukanmu,” inji shi.

Ya ce a shirye yake ya hada hannu da gwamnati saboda kafa wata cibiya da za a horar da matasa kan wannan aiki da kuma wayar da kai kan kula da lafiya ta gargajiya.

Ya ce za a iya zamanantar da magungunan gargajiya su yi goyayya da na Turawa, wadanda suka zamanantar da irin nasu