Search
Subscribe
Inteesar el-Fallatah: ’Yar fim da ta ajiye aikin ta koma bayan kyamara

Inteesar el-Fallatah riqe da kyamara yayin daukar wani fim

Inteesar el-Fallatah: ’Yar fim da ta ajiye aikin ta koma bayan kyamara

Halima Abdulkadir Adam wacce aka fi sani da Inteesar el-Fallatah, jaruma ce a masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood, a kwanakin nan ta koma bayan kyamara, inda take burin zama babbar darakta. A hirar da Aminiya ta yi da ita a ranar Litinin da ta gabata, jarumar ta bayyana dalilin da ya sa ta shiga harkar fim, kalubalen da take fuskanta da kuma dalilin da ya sa take ta zama kwararriyar darakta a duniya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Mene ne takaitaccen tarihinki?

Sunana Halima Abdulkadir Adam, amma an fi sanina da Inteesar el-Fallatah, an haife ni a Kano, a Kano na yi karatuna, nan na girma, yanzu ma a Kano nake zaune. Ta fannin karatu na yi firamare da sakandare a Kano, a yanzu kuma a watan Agusta Insha Allahu zan kammala karatun digirina a kwas din Harkokin Kasashen Waje (International Relations).

Me ya ja hankalinki kika shiga harkar fim?

A gaskiya a farko ban dauka zan yi fim ba, inda bayan na fara, sai na ga zan iya harkar. A da ba kamar yanzu ba, ana cewa duk macen da take fim ana yi mata kallon ’yar iska, sunanta ya baci, ba za a darajata kamar yadda za a daraja kowace mace da ba ta fim ba, ana ganinta da wani tambari na daban. Ni kuma sai nake ganin bai kamata ba, sai na ce to zan iya shiga fim kuma in na shiga fim zan nuna ba fa kowace mace da ta shiga fim ba ne ta baci.

Yaya kika samu kanki a harkar fim?

Jarumi Nuhu Abdullahi aminina ne, muna mutunci da shi sosai, bayan na yi sha’awar shiga harkar sai na yi wa Nuhu magana, shi kuma sai ya hada ni da furodusa Abdul’Aziz Dansmall, bayan ya hada ni da shi ne na fara fitowa a fim, inda na fito tare da jaruma Asma’u Nas cikin wani fim mai suna ‘Raihan.’

A bangaren gida shin ba ki fuskanci kalubale ba lokacin da kike ce za ki fara harkar fim?

A lokacin da na fara babu wanda ya sani a gidanmu, sai bayan na fara ne, na fara tunanin yanzu yaya zan yi in fada a gida. Daga baya tun da na riga na fara sai suka ji, kuma dama su ma sun rika fadar idan mace ta fara harkar fim ai shi ke nan ta daina zama a gida, sai suka ga ina harkar kuma ina zaune a gida.

A lokacin da aka ji a gida mahaifiyarmu ce ta fi daga hankalinta, ta rika cewa na bata sunana. Na ce mata abin da ake cewa idan mace ta shiga fim sunanta ya baci ba haka ba ne. Na ce kuma ta bari ta ga idan har ta ga na aikata wani kuskure sai ta yi magana. Bayan na fara harkar fim sai suka ga ina zaune a gida, idan aiki ya tashi sai a ga na je, wani lokaci ma ba na zuwa lokeshan ni kadai, duk lokeshan din da nake zuwa za ka ga ’yan gidanmu a wurin, wani lokaci ina zuwa da kanena ne.

Zuwa yanzu kin yi fina-finai kamar nawa?

A gaskiya da ina kirgawa amma a yanzu na manta, a cikin fina-finan da na fito akwai, ‘Asiya’ da ‘Halin Mace’ da ‘Abin Sirri Ne’ da sauransu.

Yaya kika ji a rana ta farko da za a fara dora miki kyamara?

Har na je lokeshan din fim din ban yarda cewa zan fara fitowa a fim ba, duk da cewa an ba ni ‘script’ sai nake ji kamar ba zan iya ba. Amma bayan an girka kyamara da an kunna haske (light) an kuma yi mini kwalliya (make up), sannan bayan daraktan fim din Ali Gumzak ya ce ‘action’ sai na fara zuba, ban tsaya ba sai da aka ce ‘cut.’

Za mu iya cewa ba ki yi rawar jiki ba ke nan?

A gaskiya ban yi ba, saboda ina da gogewa a rayuwa da kuma yarda da kaina ‘confidence’, don haka ban ji wata fargaba ko na yi rawar jiki ba.

A cikin fina-finan da kika yi wanne ya fi ba ki wahala?

Fim din ‘Asiya’ ya fi ba ni wahala saboda an dade ana daukar fim din, a yi gaba a dawo baya, haka a rika yi, inda hakan kuma ya ba ni wahala.

A yanzu a matsayinki na jaruma wane kalubale kike fuskanta?

Babban kalubalen da nake fuskanta shi ne yadda mutane suke yi mana kudin goro, ba su san halin mutum ba, amma su rika yin kudin goro suna mana kallon ’yan iska, babban kalubalen ke nan.

Yanzu an ga kin mayar da hankali wajen rike kyamara, me ya ja hankalinki ki koma wannan bangare?

Bayan na fara fitowa a fim sai na ga kyamara ta fi burge ni sai na ji na fi son tsayawa a bayan kyamara, sai na yi magana da Murtala Balala na ce masa ina so in zama darakta. Sai ya karfafa mini gwiwa ya ce zan iya, wadansu mutanen da suke wurin a lokacin da na yi maganar suna ta dariya, suna cewa ba zan iya ba. Ni kuma na ce musu zan iya, muka zauna muka yi magana, ya fahimci da gaske nake, sai ya fara koya mini amfani da kyamara.

Bayan kin fara aiki da kyamara, ko an taba kiranki wani aiki?

A yanzu dai zan ce na gama koya don har na sayi kyamara, kuma idan an kira Balala aiki tare muke zuwa, amma yanzu akwai ayyukan da zan je, daya kam ma a Nollywood ne.

Ko ’yan Kannywood sun yi miki wani irin kallo da kika ce kina son zama mai daukar fim da kyamara ba?

Mutane suna ta maganganu, suna cewa wai ita wannan da me ta zo, ga ta jaruma, ga kyamara, ga shi tana son zama darakta, mutane suna ta magana, amma dai hakan bai sa na karaya ba.

A lokuta da dama mutanen da suke aiki da kyamara ana bukatar su sanya kananan kaya, ga guje-guje da sauransu, amma kuma a wasu hotunan da kika fitar an ganki sanye da atamfa har da gyale, kina ganin wadannan kaya za su ba ki damar aikin ba tare da takura ba?

Idan na sa wando da riga na fi sakewa, saboda a dauki kyamara daga nan a mayar da ita can, amma zan iya sa atamfar idan fim din a falo ne ko kuma wurin da ba zai bukaci guje-guje ko zirga-zirga ba.

Jama’a suna yi miki kallon macen da ke jin dadi, wacce ba za ta so shan wahala ba, amma aiki da kyamara yana bukatar guje-guje, shin kina ganin kin shirya yin haka din?

To, gaskiya abin da na dauka a kaina shi ne duk abin da na dauka zan yi, to zan iya, shi ya sa duk wahalar abu idan na ce zan yi, to zan yi, duk wani abu da ake bukata a yi yayin daukar fim da kyamara to na shirya zan yi haka.

Wane buri kike so ki cimma a harkar fim?

Yanzu babbar burina in zama babbar darakta, saboda aktin bai fiye burge ni ba, amma ka ga na iya kyamara, kuma mutum ba zai zama babban darakta ba sai ya iya kyamara.

A karshe ko wane kira kike da shi ga al’umma?

Ina so gwamnati da kamfanoni da sauran masu hannu da shuni su rika taimaka wa mata da kananan sana’o’i, sannan a tashi tsaye don a magance barace-barace na almajirai da barace-baracen da mutanenmu na Arewa suke yi, masu bara sun yi yawa. Ina son mutanen Arewa su taso a hada kai don a daga darajar arewa a duniya.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin